Aminu Ado Bayero

Babbar Kotun Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta hana Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin sarki, tare da bai wa ‘yan sanda umarnin fitar da shi daga gidan sarki da ke Nasarawa.

A ranar Litinin ne Babbar kotun ta fadi hakan a cikin wani umarni da ta bayar a kan dambarwar da ke faruwa a Masarautar Kano tun a makon da ya gabata, bayan sauke Sarki Aminu da sauran sarakunan jihar hudu da kuma naɗa Sarki Muhammadu Sanusi a matsayin sarki ɗaya tilo a faɗin jihar.

Umarnin kotun, ya fito ne bayan shigar da ƙara da Atoni Janar da majalisar dokoki na jihar Kano suka yi kan sarakunan biyar da aka soke na Kano da Gaya da Rano da Ungogo da Bichi da Sufeto Janar na ‘yan sanda da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya da shugaban hukumar Civil Defense.

A cikin umarnin wanda TRT Afrika Hausa ta samu gani, kotun ta bayyana matakai biyar da ta ɗauka kan lamarin da suka haɗa da:

  • An hana dukkan sarakunan nan biyar da aka sauke ko fadawansu ko bayinsu bayyana kansu a matsayin masu sarauta har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da aka shigar a kansu
  • An bai wa kwamishinan ‘yan sanda umarnin ƙwace iko da fadar Sarkin Kano da ke unguwar Nasarawa
  • Kotu ta hana sarakunan biyar bayyana kansu a matsayin sarakuna don a samar da zaman lafiya a jihar Kano
  • An bai wa kwamishinan ‘yan sanda umarnin tabbatar da wadannan dokoki
  • Za a fara saurarin wannan ƙarar ranar 11 ga watan Yunin 2024

A cikin makon da ya gabata ne Majalisar Dokokin Kano ta yi doka inda ta rushe masarautun jihar biyar waɗanda gwamnatin baya ta samar.

Bayan haka ne gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano a ranar Juma'a.

Sai dai ranar Juma'a da tsakiyar dare ne Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu da ke Kano, daga nan ya zarce Gidan Sarki na Nasarawa, wanda ke da nisan kimanin kilomita ɗaya daga Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Wannan dalili ne ya sa jama'a suka soma zargin cewa yana so ya koma kan kujerarsa ta sarauta.

Sai dai a karon farko bayan ya koma kan karagar mulki, Sarki Muhammadu Sanusi ya yi zaman fada da safiyar Asabar.

Sarkin ya hau doki daga cikin gida zuwa fada domin zaman, inda mutane ke binsa suna sowa da nuna goyon bayansu a gare shi.

Wasu daga cikin hakimai na Kano sun je sun miƙa gaisuwa ga sarkin, inda shi ma Sarki Aminu ya cigaba da karɓar gaisuwa daga wasu fadawansa, lamarin da ya sanya Kano cikin ruɗani na kasancewar wataƙila sarakuna biyu a lokaci guda.

TRT Afrika