An shafe shekaru ana fama da matsalolin tsaro a Libiya. / Hoto: Reuters

Babban Bankin Libiya ya dakatar da ayyukansa bayan an yi garkuwa da wani babban jami’insa.

A wata sanarwa da ya fitar, bankin wanda yake a Tripoli ya bayyana cewa an yi garkuwa da daraktansa Musab Moslem a wajen gidansa a ranar Lahadi da safe.

Bankin ya bayyana cewa akwai jami’ansa da dama waɗanda aka yi barazanar sace su.

“Mun dakatar da aikinmu kuma ba za mu ci gaba ba har sai an sako Moslem,” kamar yadda bankin ya bayyana a ranar Lahadi.

Matsalar siyasa

Matakin ya biyo bayan wata sanarwa da majalisar dokokin kasar Libya mai hedkwata a gabashin Libya ta fitar, inda ta yi tir da abin da ta kira yunkurin wasu mutane na karbe ikon babban bankin kasar.

Libya dai ta kasance cikin rudani tun shekara ta 2011, lokacin da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi bayan shekaru arba'in yana mulki.

A halin yanzu dai kasar na karkashin gwamnatoci biyu ne masu gaba da juna: gwamnatin hadin kan kasa da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita karkashin jagorancin Abdul Hamid Dbeibeh a birnin Tripoli mai iko da yammacin kasar da kuma gwamnatin Osama Hammad da majalisar dokokin kasar ta nada, wadda ke gudanar da ayyukanta a wajen Benghazi kuma tana mulkin yankin gabas da wasu sassan kudanci.

Kokarin da Majalisar Dinkin Duniya ke na jagorant gudanar da zabukan ‘yan majalisa da na shugaban kasa ya ci tura, lamarin da ya kara tsawaita dambarwar siyasar kasar da kuma ta’azzara matsalar tsaro a kasar mai arzikin man fetur.

AA