Hukumar tace finafinai ta Nijeriya (NFVCB) ta ce ba za ta amince da ayyukan da ke zubar da ƙima ko darajar wani addini ko al'ada ko kuma ƙabila ba a finafinai da ake shiryawa a ƙasar.
Hukumar ta bayyana haka ne bayan wasu 'yan ƙasar musamman waɗanda ke amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta korafe-korafe game da wani fim da ake shirin fitarwa a ƙasar inda aka yi amfani da Hijabi wajen nuna munanan halaye.
Lamarin dai ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta inda mafi yawan mutane musamman Musulmai suka yi ta sukar fim ɗin, suna masu kira ga NFVCB da furodusoshin shirin kan su mutunta addinin Musulunci wajen cire duk wani wuri da aka nuna Hijabi a yanayi mara kyau.
''Bai kamata a yi amfani da tufafin da Musulmai mata ke sanyawa don ado ba a fim, musamman a wuraren da aka alaƙanta shi da munanan halaye,'' kamar yadda Bashir Ahmad, tsohon mai ba wa tsohon shugaban Nijeriya ya rubuta a shafinsa na X.
''Amfani da Hijabi a irin wannan yanayi tamkar wulaƙanta iyaye da 'yan uwanmu da kuma 'ya'yanmu mata ne, wannan suturar tana nuna alamar girmamawa ne don haka siffanta ta a hanyar da ta nuna akasin haka zai yi matukar ɓata ran waɗanda suke sanya ta,'' a cewar Adiba-hayah a cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram.
''Wannan suturar tana nuna alamar girmamawa, kana siffanta ta a hanyar da ta nuna akasin haka yana ɓata wa waɗanda suke sanya ta don dalilai na addini,'' wani Sulaiman musa ya wallafa a shafin instagram.
A sanarwar da NFVCB ta fitar ta bayyana cewa ta ƙarbi ƙorafe-ƙorafe game da batun kuma tuni ta soma ɗaukar mataki.
Hukumar ta ce ''bincikenmu ya nuna cewa ba a fitar da fim ɗin a kasuwa ba balle a miƙa shi ga NFVCB don tantacewa kamar yadda doka da kuma tsare-tsarenmu suka tanadar, duk da haka mun samu damar isa ga masu furodusoshin fim ɗin kuma mun ɗauki matakai don magance ƙorefe-ƙorefen al'umma game da shirinsu."
Ta ƙara da cewa "NFVCB ba za ta bar duk wani fim ko bidiyo, ciki har da gajerun bidiyoyi da ya zagi ko wulaƙanta duk wani addini ko al'ada ko ƙabila ba."
''Za mu ci gaba da sadaukar da ayyukanmu don samar da ingantaccen canji a al'ummar Nijeriya ta hanyar tace finafinai da shirye-shiryen bidiyo," in ji hukumar.
Hukumar tace finafinan ta Nijeriya ta ce, ''Manufarmu ita ce samar da daidaito tare da kiyaye 'yancin faɗin albarkacin baki kamar yadda doka ta tanadar tare da rage take haƙƙi a zamantakewa da al'adu kuma da addini da finafinai ke haifarwa.''