A shekarar 2019 tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kirkiri masarautu hudu sannan ya nada Sarki Aminu Ado Bayero kan sarautar Kano a 2020. Hoto/ Fadar shugaban Nijeriya

Gwamnatin Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce kawo yanzu ba ta yanke shawara game da sabbin masarautun da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya kirkira ba.

Wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, kakakin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya fitar ranar Laraba ta musanta "rade-radin" da ake yi a soshiyal midiya game da soke masarautun da tsohon gwamnan ya kirkira.

A watan Mayun 2019 ne tsohon Gwamna Ganduje ya kirkiri masarautu hudu: Rano da Karaye da Gaya da kuma Bichi.

Ya kirkiro su ne a yayin da takaddama ke faruwa tsakaninsa da tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, wanda ya zama Sarkin Birnin Kano kuma daga bisani ya tsige shi daga kan sarauta a 2020.

Lamarin ya jawo matukar ce-ce-ku-ce da raba kawunan al'ummar jihar.

Sai dai tun da Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben gwamna a watan Fabrairu ake ta rade-radin cewa zai rusa masarautun sannan ya dawo da tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II.

Kazalika a wata hira da aka yi da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, uban gidan sabon gwamna a watan Afrilu, ya ce alhakin dawo da tsohon sarkin yana hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf.

“Mun yi kokari ba mu sanar da maganar sarki - ko za a cire ko za a sa ko za a yi kaza ba, amma yanzu ka ga dama ta samu, su wadanda Allah ya bai wa wannan ragama su za su zauna... Za su je su duba su gani mene ne ya kamata su yi a halin da suka samu kansu,” kamar yadda tsohon sanatan a Nijeriya ya bayyana a wancan lokacin.

Tattaunawa a fili

Sai dai sanarwar da Sanusi Dawakin Tofa ya fitar ta ce "sabanin rade-radin da ake yadawa a soshiyal midiya, har yanzu gwamnatin Kano ba ta dauki mataki kan sabbin masarautun ba.

"Tattaunawar da za a yi tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar dokoki za ta kasance ta a fili domin bai wa jama'ar Kano samun bayanai game da manyan manufofi da matakan gwamnatin NNPP," in ji sanarwar.

Ta kara da cewa gwamnan jihar ya mika bukatarsa ta nada masu ba shi shawara 20 wadanda majalisar dokoki ta amince da su a zamanta na farko ranar Laraba.

Ana sa ran mika jerin sunayen kwamishinonin da za su yi aiki da gwamnan zuwa majalisar dokoki don tabbatar da su a makon gobe, in ji Sanusi Dawakin Tofa.

TRT Afrika