Tinubu ya dauki matakai da dama ciki har da cire shugaban hukumar EFCC daga kan mukaminsa./Hoto:Fadar shugaban Nijeriya

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya ta ce ba ta gudanar da bincike kan shugaban kasar Bola Tinubu game da zargin cin hanci.

Wata sanarwa da hukumar ta Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) ta wallafa a shafinta na intanet ranar Asabar ta musanta rahoto da wata jaridar da ake wallafawa a intanet ta yi cewa kwanakin baya jami'an tsaro na DSS sun kwashe fayil-fayil da ke zargin shugaban kasar da cin hanci da ke ajiye a hukumar yaki da rashawa ta kasar.

ICPC ta ce “babu wasu fayil-fayil a hedikwatarmu ko ofisoshinmu da ke fadin Nijeriya da ke zargin Shugaba Tinubu ko masu ba shi shawara.”

“Zargin da ake yi cewa an kwashe fayil-fayil daga hukumar ba shi da kanshin gaskiya kuma ya kamata mutane su yi watsi da shi,” in ji sanarwar ta ICPC.

Hukumar ta bukaci 'yan jarida su “daina watsa labaran karya da kuma wadanda wasu da ke da mugun nufi ke daukar nauyin watsa su.”

Tinubu, wanda ya karbi mulki ranar 29 ga watan Mayu, ya sha alwashin magance matsalar cin hanci da rashawa.

Tun lokacin da aka rantsar da shi, ya aiwatar da sauye-sauye da dama ciki har da cire shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta'annati ta EFCC.

TRT Afrika