Tun bayan da aka yi juyin mulki a Nijar, an gudanar da zanga-zanga daban-daban domin nuna goyon baya ga sojojin kasar. Hoto/Getty Images

Har yanzu ba san inda jakadan Faransa a Jamhuriyar Nijar Sylvain Itte yake ba, kwana biyu bayan shugaban kasar Emmanuel Macron ya sanar cewa zai janye shi daga kasar cikin awanni kadan.

A wani mataki na ba kasafai ba, ranar Lahadi Macron ya ce Faransa za ta janye dakarunta 1,500 da ke Nijar watanni biyu bayan takaddama ta ki ci ta ki cinyewa tsakaninsa da sojojin kasar wadanda suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Faransa ta ki amincewa da sabuwar gwamnatin sojin Nijar kuma Macron ya yi zargin cewa sun yi garkuwa da jakadansa a kasar.

Tun bayan juyin mulkin, sojojin sun soke kawancen tsaro da ke tsakaninsu da Faransa sannan suka umarci jakadanta ya fita daga kasar bayan sun soke izininsa na zama a Nijar.

Macron ya ce yana so ya janye 'yan kasar tasa daga Nijar cikin lumana. Ranar Litinin sojojin Nijar sun ce suna so a tsara jadawalin ficewar dakarun Faransa daga kasar.

Sai dai majiyoyin diflomasiyya na Faransa sun ce sun yi amannar sojojin da suka yi junyin mulki a Nijar suna yin amfani da jakadan Faransa da tawagarsa domin yi wa kasarsa mugun wulakanci.

Tuni dai Faransa ta janye dakarunta daga Mali da Burkina Faso da ke makwabtaka da Nijar, inda a yanzu ba ta da jakadu.

Itte, wanda shahararren ma'aikacin jakadanci ne wanda a baya ya rika yaki da labaran karya a nahiyar Afirka, yana fuskantar kalubale na ganin yadda kimar kasarsa ke ci gaba da zubewa.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun kori jakadan Faransa daga kasar

An kwashe makonni da rufe ofishin jakadancin sakamakon jerin zanga-zangar da 'yan Nijar suke yi, lamarin da ya matsa lamba kan Paris domin ta janye jakadanta daga Nijar, ko da yake a baya Macron ya sha cewa ba za ta sabu ba.

Majiyoyi sun ce an katse wutar lantarki da ruwa a foshin jakadancin na Faransa.

Ba a ga wata alamar motsi ba a ofishin jakadancin a ranar Talata.

Da aka tambaye ta game da makomar jakadansu a Nijar, kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Faransa Anne-Claire Legendre ta ki cewa uffan game da yadda zai koma gida, sannan ba ta ce komai ba kan ko an samu matsala game da tafiyarsa.

Sannan ta ki cewa komai kan ko har yanzu yana Nijar da kuma adadin ma'aikatan jakadancin da har yanzu suke ofishin jakadancinsu na Yamai.

Sai dai Legendre ta shaida wa taron manema labarai da take gudanarwa a kullum cewa: "Ba za mu bari sojojin da suka yi juyin mulki su yi garkuwa da mu ba".

Ma'aikatan diflomasiyya sun ce ofisoshin jakadanci suna da kayayyaki na ko-ta-kwana da fetur da injin janareto na ko-ta-kwana ko da yake za su iya daina aiki, lamarin da zai kara matsa lamba kan Paris don ta biya bukatun sojojin Nijar.

Reuters