Ministan harkokin wajen Burkina Faso ya jinjina wa irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Burkina Faso da Rasha a ranar Asabar inda ya ce ta "wuce" alaƙar da ƙasar ke da ita da Faransa a baya.
Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2022, ƙasar Burkina Faso ta yanke dangantaka da Faransa, inda ta rungumi kasar Rasha, wadda ta aike da kwararrun sojoji don taimaka wa Ouagadougou yaki da ‘yan tawaye.
Ministan harkokin wajen Burkina Faso Karamoko Jean-Marie Traore ya halarci taron ƙasashen Afirka da Rasha a birnin Sochi da ke kudancin Rasha, inda ya ce "Rasha abokiya ce da za mu iya samun ci gaba da ita" kuma babu "fargabar" dogaro da karfin soji kan Moscow.
"Wannan tayin da aka yi ta hanyar hadin gwiwa da Rasha, ya fi dacewa ga al'ummar Burkina Faso," kamar yadda ya shaida wa AFP a wata hira da aka yi da shi a gefen taron na Sochi.
Faɗaɗa diflomasiyyar Rasha
Ya bayyana cewa Rasha kamar Burkina Faso, ta sha fama da "maganganu waɗanda sauran ƙawaye" na Yamma ke yi a kanta.
Rasha dai na neman ci gaban diflomasiyya da siyasa da tattalin arziki a Afirka yayin da dakarunta ke yaki a Ukraine.
Batun da Rasha ke yawan yi na sabon salon mulkin mallaka lamari ne wanda ya zo daidai da tunanin shugabannin Afirka da dama.
Burkina Faso ƙasa ce wadda Faransa ta yi wa mulkin mallaka tsawon fiye da shekara 60, inda dangantaka ta taɓarɓare tsakanin ƙasar da Burkina Faso tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a 2022.
Dogaro da Moscow
Moscow ta aike da malamai masu horaswa na soji zuwa Burkina Faso - da kuma wasu kasashen Afirka da dama - don taimakawa a yakin da aka kwashe shekaru fiye da goma ana yi da masu tayar da kayar baya.
Minisitan Harkokin Wajen na Burkina Faso Karamoko Jean-Marie Traore ya yi watsi da maganganun da ake yi kan cewa ƙasar na son ta dogara baki ɗaya kan Moscow.
"Babu wannan batun, saboda mun san abin da muke so da kuma inda muke son zuwa. Kuma mun san yadda muke son yin aiki tare da sabbin ƙawayenmu" kamar yadda ya shaida wa AFP.