Masu sharhi a harkokin siyasa na cewa ganawar  Atiku da Kwankwaso wani bangare ne na siyasar Nijeriya da 'babu masoyi ko makiyi na dindindin'./Hoto: @RMKwankwaso

Tsohon dan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP Sanata Rabiu Kwankwaso ya karbi bakuncin takwaransa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar a gidansa da ke Abuja ranar Talata da daddare.

"Na ji dadin karbar bakuncin dan uwana, tsohon mataimakin shugabana Najeriya, mai girma Alhaji Atiku Abubakar a gidana da yammacin nan. Ina godiya ga Waziri bisa wannan ziyara ta 'yan uwantaka," in ji Sanata Kwankwaso a sakon da ya wallafa a shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter.

Bai yi karin bayani game da dalilin ziyarar ba. Sai dai wannan ne karon farko da tsoffin 'yan takarar biyu - wadanda suka yi hamayya sosai gabani da kuma yayin zaben 2023 - suka yi irin wannan ganawa.

TRT Afirka ta kira Kwankwaso ta wayar tarho domin karin bayani, sai dai bai amsa kiran ba kuma kawo yanzu bai turo mana amsar sakon da muka aika masa ba.

Amma wasu rahotanni sun ce manyan 'yan siyasar biyu sun gana ne kan rawar da za su taka wajen ci gaban kasar musamman ganin yadda 'yan Nijeriya suke kara fuskantar matsin rayuwa sakamakon wasu matakai da gwamnati ke dauka.

Atiku Abubakar ne ya zo na biyu yayin da Sanata Kwankwaso ya zo na hudu a zaben shugaban kasar Nijeriya na 2023 wanda Bola Tinubu ya lashe.

Tsohon mataimakin shugaban kasar da kuma takwaransa na jam'iyyar LP, Peter Obi, sun garzaya kotu inda suke kabulantar zaben. Sai dai Sanata Kwankwaso bai kai kara kotu ba.

Hasalima bayan zaben tsohon gwamnan na Kano ya gana da zababben shugaban kasar Bola Tinubu a Paris inda ya ce sun tattauna kan yadda za su kafa gwamnatin hadaka. Amma daga bisani wasu bayanai sun ce ya fasa hada kai da gwamnati mai ci.

Adawa ta yi zafi sosai tsakanin Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso - wanda a baya yake cikin jam'iyyar PDP - sakamakon rikicin da ya barke a jam'iyyar wanda ya sanya shi fita daga cikinta ya koma NNPP inda ya yi mata takarar shugaban kasa.

A wancan lokacin Sanata Kwankwaso ya dora alhakin rikicin siyasar kan kokawar da wasu manyan 'yan PDP suke yi na ture shi daga cikinta don Atiku ya samu damar tsayawa takara a karkashin jam'iyyar.

Masu sharhi a kan harkokin siyasa na cewa ganawar Atiku da Kwankwaso wani bangare ne na siyasar Nijeriya da 'babu masoyi ko makiyi na dindindin'.

TRT Afrika