Atiku Abubakar ya koka kan barazanar da ya yi zargin cewa masarautun gargajiya na fuskanta a Nijeriya. / Hoto: Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya zama dole a kare masarautun gargajiya daga irin barazanar da suke fuskanta daga wasu gwamnonin jihohi masu ƙarfi.

Dan takarar shugaban Nijeriyar a zaɓen 2023 ya bayyana haka ne a daidai lokacin da wasu gwamnoni a ƙasar ke ƙoƙarin kawo sauyi a tsarin masarautun jihohin masu ɗumbin tarihi.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a shafinsa na X, Wazirin na Adamawa ya ce zai yi wuya a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma idan aka kawo cikas a tsarin naɗa sarakunan gargajiya.

Atikun ya yi kira da a kawo sauyi ga kundin tsarin mulki ba wai wanda zai amince da zaman sarakunan gargajiya kawai ba, amma wanda zai tsara irin ayyukan da ofisoshinsu za su rinƙa gudanarwa.

“Ina so a tuna cewa sarakunan gargajiya su ne suka assasa tsarin gwamnati tun kafin zuwan masu mulkin mallaka.

“Haka kuma sun yi mulki lafiya lau. Sakamakon haka, ya kamata mu kare su da alkinta su ba wai lalata su ba. A kan haka ne nake kira da a yi gyara ga kundin tsarin mulki wanda ba wai wanda zai amince da zaman sarakunan gargajiya kawai ba a doka, amma wanda zai tsara irin ayyukan da ofisoshinsu za su rinƙa gudanarwa,” in ji sanarwar.

A Jihar Kano, an ga yadda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rushe masarautu biyar na Jihar inda ya naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, duk da cewa ana ta ɗauki ba daɗi a kotu tsakaninsa da Aminu Ado Bayero wanda har yanzu ya ƙi fita daga Kano tare da dagewa kan cewa har yanzu shi ne sarki.

Haka kuma a makon nan Ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Musulmai ta MURIC ta yi zargin cewa Gwamnan Jihar Sokoto na yunƙurin tsige Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar II.

Shi ma Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ana zargin yana zaman doya da manja tsakaninsa da Oba Ewuare II wanda shi ne Oba na Benin.

TRT Afrika