Gwamnatocin soja na Burkina Faso da Mali da Nijar sun ce matakin da suka ɗauka na ficewa daga Ƙungiyar Raya Tattalin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS, abu ne da ba zai taɓa sauya ba.
Ƙasashen uku da suka kafa ƙungiyarsu ta Ƙawacen Yankin Sahel mai suna Sahel Alliance ta zargi ECOWAS da zama ‘yar ‘amshin-shata ga Faransa, wacce ita ce ta yi musu mulkin mallaka, amma a yanzu suka raba gari da ita.
Bayanin na ƙasashen uku na yankin Sahel mai fama da rikici ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyar ECOWAS take shirin gudanar da wani taro a ranar Lahadi, inda ake fatan shugabanni za su nemo hanyar da za a bi don hana ƙasashen uku ɓallewa.
Ƙasashen da suka balle ba su sanar da shirin halartar taron ba. Sun yi wani taro daban a ranar Juma'a a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar.
“Ministoci sun sake nanata matakin ficewa daga kungiyar ECOWAS yadda ba za a iya dawo da su ba, kuma sun ƙuduri aniyar bin tsarin yin nazari kan hanyoyin ficewa domin amfanin al’ummarsu,” in ji wata sanarwa ta haɗin gwiwa.
Raba gari da Faransa
Ƙasashen uku sun kafa ƙungiyar Haɗin Kan Yankin Sahel (AES), bayan sun raba gari da Faransa tare da karkata zuwa ga Rasha.
Ficewarsu daga ECOWAS na iya yin babban tasiri ga zirga-zirgar jama'a da kayayyaki ba tare da matsala ba a yankin.
‘Ƙasashen da ke ɓallewa daga ECOWAS, wadanda duk sun sojoji suka yi wa juyin mulki sannan suke fuskantar tada ƙayar baya a shekarun baya bayan nan, sun sanar da fice daga ƙungiyar ECOWAS a watan Janairu.
A ƙarkashin dokokin ƙungiyar, ficewar ta su za ta fara aiki ne shekara guda bayan sanarwar ta su a watan Janairun 2025.
Rashin jituwar su da ECOWAS ta biyo bayan barazanar tura sojoji saboda juyin mulkin da aka yi a Nijar a watan Yulin 2023 - wanda shi ne juyin mulki na shida a yankin cikin shekaru uku - tare da sanya wa ƙasar takunkumi mai tsanani, abin da ya fusata shugabannin mulkin sojoja na ƙasashen.