Magoya bayan jam'iyyar ANC riƙe da alluna da ke dauke da fuskar shugaban ƙasar Afirka ta Kudu kana shugaban jam'iyyar ANC Cyril Ramaphosa. / Hoto: AFP

Shugaba Cyril Ramaphosa ya buƙaci shugabannin jam'iyyun siyasa a Afirka ta Kudu da su haɗa kai tare da aiki tare don cimma muradun al'umma bayan da jam'iyyarsa ta ANC ta rasa rinjayen shugabancinta na tsawon shekaru 30 da ta kwashe a kan mulki a babban zaben ƙasar da aka gudanar.

Sai dai duk da wannan rashin nasara ta ANC, alamu na nuna al'amura su iya sauyawa dangane da halin da ake ciki bayan ayyana sakamakon zaben, la'akari da yadda jam’iyyar tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma ta ƙaurace wa halartar bikin sanar da sakamakon zaɓen,kazalika har zuwa yanzu ba ta fito fili ta yi na’am da sakamakon ba.

Sakamakon zaben dai ya bai wa jam'iyyar Ramaphosa ta (African National Congress) ANC mai mulki kujeru 159 a majalisar dokokin ƙasar mai kujeru 400, adadi mafi karanci da ake buƙata a babban zabe.

Jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance (DA) ta samu adadin kujeru 87, yayin da jam'iyyar tsohon shugaban ƙasar Zuma ta uMkhonto weSizwe (MK) ta samu kujeru 58, sai jam'iyyar Economic Freedom Fighters (EFF) mai fafutukar dawo da kimar tattalin arziki ta Julius Malema ta samu kujeru 39, sai kuma wasu kananan jam’iyyu da suka samu kujeru daban-daban a zauren.

Gwamnatin haɗin-gwiwa

Adadin kuri'un da jam'iyyar marigayi Nelson Mandela ta samu ya ragu da kashi 40 daga kashi 57 cikin 100 da ta samu a shekarar 2019.

Sabuwar majalisar da aka zaɓa za ta yi zama cikin makonni biyu kan aikinta na farko da za ta mai da hankali a kai shi ne zaben shugaban ƙasa wanda zai kafa sabuwar gwamnati a Afirka ta Kudu.

Babu wanda ya taba ƙarbe mulki daga hannun Jam'iyyar ANC tun bayan da Afirka ta Kudu ta koma mulkin dimokuradiyya daga mulkin wariyar launin fata, yanayin da a karon farko ke nuni da cewa sai jam'iyyar ANC ta buƙaci goyon bayan wasu jam'iyyu don sake tabbatar da zaben Ramaphosa a matsayin shugaban ƙasa.

A jawabin da ya yi bayan bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen a hukumance da aka yi a ranar Lahadi, Ramaphosa ya nuna ƙwarin gwiwar da yake da shi bisa wata yarjejeniya ta haɗaka, sai dai ya jaddada buƙatar samun haɗin kai daga dukkan jam'iyyu don mutunta sakamakon zaɓen da kuma aiki tare.

AFP