Masu sharhi a kasar Kenya sun yi Allah wadai da hanyoyin da 'yan sandan kasar suka bi wajen dakile zanga-zangar adawa da gwamnati a ranar Litinin.
Da yake magana da sashen TRT Afrika, wani mai sharhi kan siyasa da gwamnati Martin Andati ya ce cin mutuncin da ‘yan sanda suka yi wa masu zanga-zanga bai dace.
Gamayyar kawance ta Azimio la Umoja-One ta Kenya da jagoran hamayya Raila Odinga ne suka jagoranci zanga-zangar a ranar 20 ga watan Maris don nuna adawa da gwamnatin William Ruto da kuma tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar.
Sai dai Ministan Harkokin Cikin Gida na Kenya, Farfesa Kithure Kindiki, ya jinjina wa ‘yan sandan bisa kokarinsu na shawo kan jerin zanga-zangar adawa da gwamnati da aka gudanar.
Ministan ya shaida wa ‘yan sandan cewa “muna alfahari da ku!”
An yi ta kai ruwa rana tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga lamarin da ya kai ga fesa ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye tare da kama mutane, yayin da bata-gari suka yi ta lalata dukiyoyi da sace-sace a wasu yankunan.
Mafi yawan hanyoyin da za su sada mutane da babban birnin sun cunkushe ta yadda mutane ba sa iya wucewa, tare da tsayar da al’amura cak.
Tun da safiyar ranar ‘yan sanda suka yi ta kokarin shawo kan lamarin da kuma dakatar da zanga-zangar.
Sai dai isar Raila Odinga wajen da rana ta jawo zanga-zangar ta yi kamari. ‘Yan sanda sun yi ta jefa hayaki mai sa hawaye don tarwatsa taron.
Rahotannin sun ce ‘yan sanda sun harbe wani dalibin Jami’ar Maseno, William Mayenga a gundumar Kisumu, a ranar Talata.
Sai dai Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar Kithure Kindiki ya wallafa sako a shafinsa na Tuwita yana yabon ‘yan sandan kan yadda suka murkushe masu zanga-zangar.
“Hukumar ‘yan sanda ta zama abar alfaharinmu, ganin irin kokarin da ta yi wajen shawo kan zanga-zangar da aka yi tsawon yini guda a kasar.
“Dole ne Kenya ta shawo kan yadda ake keta doka tare da tabbatar da cewa an bi kundin tsarin mulki, don samar da tabbataccen zaman lafiya a yankinmu,” kamar yadda ya wallafa.
Sakataren ya kara da cewa dole ne kowane dan kasa ya bi doka.
Wannan lamari na zuwa ne kwana guda bayan da William Ruto ya yi Allah wadai da zanga-zangar yana mai nanata cewa gwamnatinsa ba za ta yarda a karya doka ba.
Mataimakin shugaban kasa Rigathi Gachagua ya ce jerin zanga-zangar sun sa kasar ta yi asarar kusan dala miliyan biyu.
Amma mai sharhi kan siyasa Mr Andati yana ganin hakan ba hujja ba ce da za ta sa 'yan sanda su dauki tsattsauran mataki a kan fararen hula.
“Me ya sa za su yi ta harba hayaki mai sa hawaye? Ba su da wata kwarewa kamar yadda ake tsammani, kuma abin da suka yi din bai kamata ba.
"Ku kwatanta da abin da ya faru a Afirka ta Kudu. ‘Yan sanda ne suka dinga yi wa masu zanga-zanga rakiya. Ba a samu faruwar irin haka ba,” ya ce.
Ya kuma ce irin wannan fito na fito tsakanin Shugaba William Ruto da bangaren hamayya za ta ci gaba da faruwa don haka dole ne ‘yan Kenya su shirya ganin irin wadannan zanga-zanga.
Masanin ya yi amanna cewa kasashen duniya da al’ummar Kenya ne kawai za su tursasa wa bangarori biyun sassautawa.
“Mun shirya wa doguwar adawa; abin ba zai zo da sauki ba,” in ji shi.
Duk da alkawarin da Shugaba William Ruto ya yi na cewa zai dauki kwakkwaran mataki kan irin wadannan zanga-zanga, jagoran hamayya Raila Odinga ya sha alwashin cewa za a dinga gudanar da boren a duk ranar Litinin.
Mista Odinga ya ce za a dinga hakan ne don jan hankalin Shugaba Ruto wajen magance tsadar rayuwar da ‘yan Kenya ke fuskanta.