'Yan takara 19 ne suke neman maye gurbin George Weah, wanda ya kwashe shekara biyar a kan mulki./Hoto: Reuters

Kimanin mutum miliyan 2.4 ne suke kada kuri'a ranar Talata domin zaben shugaban kasar Laberiya inda Shugaba George Weah ake neman wa'adi na biyu bayan ya kwashe shekara biyar a karagar mulki a kasar da ke fama da zargin cin-hanci da tabarbarewar tattalin arziki.

Weah, mai shekara 57, wanda fitaccen dan kwallon kafa ne da ya rikide ya zama dan siyasa, ya ce yana bukatar karin lokaci domin cika alkawuran da ya dauka na gyara fannin tattalin arzikin kasar da hukumomi da kuma inganta abubuwan more rayuwa da suka hada da hanyoyi.

An zabe shi a 2017 a matsayin shugaban farar-hula na farko na kasar cikin shekara fiye da 70, sai dai a yanzu Weah yana fuskantar kalubale daga 'yan takara 19 da ke neman maye gurbinsa.

Dole ne dan takara ya samu akalla kashi 50 na kuri'un da aka kada idan ba haka ba sai an je zagaye na biyu a zaben.

Labari mai alaka: Dalilin da ya sa zaben Liberia na 2023 yake da muhimmanci yayin da Weah yake fuskantar kalubale

A yayin da yake kammala yakin neman zabensa ranar Lahadi a birnin Monrovia, Weah ya ce ya samu nasarori da dama a wa'adinsa na farko duk da tarin kalubalen da ya fuskanta.

Babban mai kalubantar Weah shi ne tsohon mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai, mai shekara 78, wanda ya sha kaye a zaben 2017. Boakai ya sha alwashin ceto Laberiya daga hannun wadanda ya kira masu almubazzaranci na gwamnatin Weah.

TRT Afrika