Masu zabe a ranar Lahadi za su fita domin jefa kuri’ar raba gardama kan kundin tsarin mulki a Chadi, wanda wani muhimmin mataki ne na mayar da mulki ga farar hula.
‘Yan adawa da dama ne da kuma kungiyoyin farar hula a kasar da ke tsakiyar Afirka ke kira da a kaurace wa zaben.
Masu kira kan a kaurace wa zaben na zargin cewa wannan zaben ya yi kama da wata hanya wadda ta za tabbatar da Itno da “zuri’arsa” sun ci gaba da mulki bayan shafe shekara 30 suna mulkar kasar.
Sai dai masu goyon bayan wannan kuri’ar na da yakinin samun nasara bayan yakin neman zabe da sojojin da ke kan mulki suka yi domin yakar ‘yan adawar kasar wadanda kan su ke rabe. An soma yakin neman zaben ne tun a watan Nuwambar bara.
An ta lika fastoci a N’Djamena babban birnin na Chadi wadanda aka rubuta “Eh”, domin kawo kundin tsarin mulki na gwamnatin hadin kai.
Hadin kan kasa
Bai sha bamban da irin kundin tsarin mulkin da sojojin kasar suka yi watsi da shi ba a 2021, wanda akasarin karfin mulki a hannun shugaban kasa yake. ‘Yan adawa wadanda ke son tsarin fediraliya na da kuri’ar “A’a” a zaben.
Masu kuriar “Eh” na ganin tsarin hadin kan kasa ita ce kadai hanyar ci gaba da hada kan kasar, inda kuma tsarin fediraliya zai kara jawo ‘yan aware da kuma rikici.
Ana sa ran fitar da sakamakon zaben a karshen watan Disamba, bayan Kotun Koli ta tabbatar da sakamakon kwanaki hudu bayan kammalawa.
Manyan jami’iyyu biyu da kuma kungiyoyin farar hula na adawa da sojojin da ke mulkin kasar inda suke kira kan a kaurace wa zaben, inda ake sa ran idan masu zabe ba su fita da yawa ba hakan zai rage kima da ingancin zaben.
Kungiyoyin da ‘yan adawa sun ta lika fastoci wadanda ke kunshe da kalaman cewa “ A bar kuri’ar raba gardama” da kuma babbar kuros mai launin ja.
Tsarin mika mulki
“Duka daya ne, ko dai suna yakin neman zabe kan ‘Eh’ ko kuma ‘A’a’. Duk sun raba kudaden a tsakaninsu,” kamar yadda Badono Daigou na jam’iyyar adawa ta GCAP ya shaida.
“Sun riga un kammala zaben. Masu goyon bayan ‘Eh’ su a su ci,” in ji shi.
Mahamat Deby mai shekara 37 ya zama shugaban rikon kwarya na mulkin sojin kasar a Afriulun 2021 bayan rasuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno wanda ‘yan tawaye suka kashe a fagen daga. Mahaifin Mahamat ya jagoranci Kenya a matsayin shugaban kasa sama da shekara 30.