Nigeria na daya daga cikin manyan kawayen Turkiyya a fannin kasuwanci. Hoto/Fadar shugaban Nijeriya

A ranar Talata 2 ga watan Mayu ne ake soma taron zuba jari tsakanin Turkiyya da Nijeriya a birnin Santambul.

Zai mayar da hankali kan zamanantar da aikin gona da inganta fannin makamashi da hakar ma’adinai da man fetur da iskar gas da ababen more rayuwa.

Taron na kwanaki biyu zai karbi bakuncin manyan jami’an gwamnatin Nijeriya da ciki har da Ministar Zuba Jari da Kasuwanci ta kasar, Ambasada Mariam Katagum.

Nijeriya, wadda ke cikin kawayen kasuwanci mafi girma daga nahiyar Afirka, na daga cikin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a nahiyar mai mutum sama da miliyan 200.

Wani bincike da Jami'ar Yasar ta Turkiyya ta gudanar ya nuna cewa a shekaru 26 da suka gabata kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa Nijeriya a duk shekara sun karu da kashi 17 cikin dari daga dala miliyan 13.1 a 1995 zuwa dala miliyan 877 a 2021.

A 2021, Nijeriya ta fitar da zunzurutun kudi da ya kai dala biliyan 1.05 zuwa Turkiyya.

Manyan kayayyakin da kasar ta fitarwa zuwa Turkiyya sun hada da danyen mai na dala miliyan 518 da iskar gas ta dala miliyan 460 da sauran albarkatun mai na dala miliyan 51.4, in ji binciken.

TRT Afrika