'Yan Afirka ta kudu na zabar 'yan majalisar dokoki da su kuma za su zabi shugaban kasa. Hoto: Reuters

'Yan Afirka ta Kudu sun fara jefa ƙuri'a a zaben da ake yi wa kallon mafi muhimmanci a kasar a cikin shekaru 30, kuma wanda ka iya ɗaga martabar jaririyar dimokuraɗiyyar ƙasar zuwa wani matsayi.

Jam'iyyar ANC da ta mulki kasar tsawon shekara 30 tun bayan mulkin tsiraru farar fata ce ta fi yin shuhura a zaben na ranar Laraba.

An fara jefa ƙuri'a da misalin ƙarfe bakwai na safe inda za a kammala da karfe tara na dare, kuma mutane miliyan 27 ne suka yi rajistar zabar 'yan majalisar dokoki wadanda daga baya kuma za su zabi shugaban kasa.

"'Zaɓen Afirka ta Kudu na da muhimmanci a yanzu haka musamman ga tarihin kasar," in ji Alex Montana, wani mai nazari a kamfanin Verisk Meplecroft.

ANC na cikin rashin tabbas

Kasar da ta fi kowacce habakar tattalin arziki a Afirka ta fuskanci matsalar tattalin arziki da zamantakewa mafi muni a duniya, ciki har da rashin aikin yi da ya kai kashi 32.

Rashin daidaito wajen samun arziki da talauci da rashin ayyukan yi da ke shafar baƙaƙen fata na barazanar kawar da ANC daga kan mulki.

Bayan lashe zabuka shida a jere, ANC na da goyon bayan ƙasa da kashi 50 na jama'a, wanda hakan ya afku ba zato ba tsammani.

Jam'iyyar na iya rasa rinjaye a majalisar dokoki a karon farko, amma za ta fi kowa yawan samun kujeru.

Goyon bayan da ake nuna mata yana raguwa. A zaben 2019 ANC ta samu kashi 57 na ƙuri'un da aka jefa, shi ne sakamako mafi muni da ta taɓa samu.

TRT Afrika