Hukumomin Afirka ta Kudu sun dakatar da aikin bincike da aka kwashe tsawon sa'o'i ana yi. Hoto: NSRI/X    

Afrika ta Kudu ta dakatar da aikin bincike da ceto na wasu masunta 11 da suka bace a lokacin da wani jirgin ruwa ya nutse a gaɓar tekun ƙasar a ranar Juma'a.

Ana fargaba masuntan sun mutu.

"Ina so in miƙa saƙon ta'aziyyata ga iyalan masuntan da ke cikin jirgin su 11 waɗanda a yanzu ake kyautata zaton sun mutu," a cewar Ministar Gandun Daji da Kamun Kifi da Muhalli na Afirka ta Kudu, Barbara Creecy a cikin wata sanarwa da ya fitar.

"An sanar da iyalan masuntan da suka rasa rayukansu cewa an dakatar da binciken,'' in ji sanarwar.

Ƙoƙarin ceto

Jirgin kamun kifin ya shiga tsaka mai wuya kana ya aika da saƙo na neman agaji a ranar Juma'a kafin ya nutse cikin tekun Atlantika ta kudu mai nisan mil 30 daga tekun Cape of Good Hope.

Ƙungiyar kula da kwale-kwalen ceto ta Afirka ta Kudu ta Cibiyar aikin ceto a tekun Ƙasa, ta ce ma'aikata 20 ne a cikin jirgin da ya yi ɓatan dabo.

Wasu jiragen kamun kifi ne suka gano mutane tara daga cikin mutanen da suka nutse.

An ƙaddamar da aikin ceto na jiragen ruwa a gaɓar tekun tare da jirage masu saukar ungulu da kuma jiragen sama na Aerios Global mai zaman kansa a Cape Town, amma mummunan yanayi da rashin ganin hanya da kyau su ka sanya a kawo ƙarshen binciken.

Tuni dai aka kaddamar da aikin bincike kan musabbabin nutsewar jirgin.

TRT Afrika