Ana farautar waɗanda suka lalata mutum-mutumin shugaban Ghana

Ana farautar waɗanda suka lalata mutum-mutumin shugaban Ghana

Gina mutum-mutumin Shugaba Nana Akufo-Addo ya janyo suka inda wasu ke cewa yabon kai ne.
An yi mutum-mutumin ne domin murnanr nasasorin da shugaban ya samu.

‘Yan sanda a Ghana suna neman waɗanda ake zargi da hannu a lalata wani ɓangare na mutum-mutumin Shugaba mai barin gado, Nana Akufo-Addo, a Lardin Yammacin ƙasar.

An lalata ƙafar hagu ta mutum-mutumin da aka gina don tunawa da shugaban ƙasar kuma aka cire rubutun jikinsa, in ji wata sanarwar ‘yan sanda.

"'Yan sanda suna yin ƙoƙarin ganin an kama waɗanda suka yi wannan aika-aikar domin gurfanar da su a gaban ƙuliya," in ji sanarwar.

Shugaba Akufo-Addo ya fuskanci suka bayan ya ƙaddamar da mutum-mutumin a watan Nuwamba domin murnar cika alƙawuran da ya yi kafin ya hau ƙaragar mulki. An soke shi da yabon kai kuma rahotanni sun ce wasu mazauna yankin sun yi barazanar rusa mutum-mumin idan ya sauka daga kan mulki.

Ƙarshen wa’adi

An lalata mutum-mutumin ne ranar Litinin da safe, kamar yadda rahotanni a kafafen watsa labaran Ghana suka ruwaito.

Shugaban zai sauka daga kan mulki a watan Janairu bayan kammala wa’adi biyu na mulki.

Ɗan takarar jam'iyyar hamayya kuma tsohon shugaban ƙasa John Mahama ne ya lashe zaɓen da aka gudanar a farkon wannan watan inda ya samu kusan kashi 57 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa- ratar nasara mafi yawa cikin sama da shekara 20.

Za a rantsar da Mahama ranar 7 ga watan Janairu kuma ya yi alƙawarin bi da ƙasar sabuwar hanya.

TRT Afrika