Ma'aikatar Kiwon lafiya ta Sudan, a wata sanara, ta caccaki RSF kan "mummunan laifin" da ta aikata. / Photo: Reuters

Hukumomi a Sudan da kuma ƙungiyoyin ƙasashen duniya sun yi Allah wadarai da kisan fiye da mutum 100 da ake zargin dakarun rundunar ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces [RSF] sun yi a ƙauyen Wad al Noora da ke jihar Gezira ta Sudan.

Ƙungiyoyin sun yi kira a gudanar da bincike nan-take tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi a wannan aika-aika.

Ranar Alhamis, Majalisar Mulkin Sojin Sudan ta Transitional Sovereignty Council ta zargi dakarun RSF da aikata kisan kiyashi a ƙauyen, tana mai cewa sun kashe "mutane da dama da ba su da laifi", sai dai RSF ta ce dakarunta sun kai hari ne a sansanoni uku na sojoji da jami'an leƙen asiri.

Wata ƙungiyar tabbatar da dimokuraɗiyya mai suna Madani Resistance Committee, ta ce mutanen da aka kashe "sun zarta 104".

Clementine Nkweta Salami, Babbar Jami'ar MDD kuma shugabar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa a Sudan, a wata sanarwa ta ce: "Na yi matuƙar kaɗuwa da rahotanni kai muggan hare-hare da kuma kashe mutane da dama a ƙauyen Wad al Noora da ke Jihar al Jazirah [Gezira] ranar 5 ga watan Yunin 2024."

"Ko da yake kawo yanzu MDD ba ta da cikakken rahoto kan lamarin da ya faru jiya, akwai ƙwararan rahotanni da ke nuna an yi luguden wuta da amfani da abubuwan fashewa a yankunan da fararen-hula suke zama," in ji ta.

Salami ta yi kira a "gudanar da cikakken bincike game da abin da ya faru a Wad Al-Noora kana a hukunta duk wanda aka samu da laifi a lamarin."

Ta ƙara da cewa RSF da kanta ta fito fili ta tabbatar da cea dakarunta sun ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa a wannan yanki ranar 5 ga watan Yuni.

Ma'aikatar Kiwon lafiya ta Sudan, a wata sanarwa, ta caccaki RSF kan "mummunan laifin" da ta aikata.

TRT World