An zaɓi Thoko Didiza ta jam'iyyar ANC a matsayin sabuwar Shugabar Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu.
Tsohuwar ministar ta aikin noma ta samu ƙuri'u 284 daga sababbin wakilai 400 a ƙuri'un da aka kaɗa ranar Juma'a.
"Zan yi aiki tare da dukkan jam'iyyu don ganin mun gudanar da harkokin wannan majalisa ta hanyar da ta dace da buƙatun al'ummar Afirka ta Kudu. Na gode ƙwarai da wannan karramawa," in ji ta.
Didiza ce za ta jagoranci tantancewa da zaɓen sabon shugaban ƙasa.
Jam'iyyar ANC ta ƙulla yarjejeniyar ƙawance da jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance (DA) domin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.
TRT Afrika