An yi wa tsohon shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma daurin-talala bayan an yi masa tambayoyi game da abin da gwamnatin kasar ta bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki a karshen watan Nuwamba.
Sai dai ofishin tsohon shugaban kasar, wanda ya jagoranci Saliyo daga 2007 zuwa 2018, ya ce ba a yi masa daurin-talala ba.
Ministan Watsa Labarai Chernor Bah ya ce Koroma, wanda a ranar Juma'ar da ta gabata aka yi masa tambayoyi, an sake gudanar da bincike a kansa ranar Asabar sannan aka sake shi bisa "sharadin cewa ba zai fita daga gidansa ba".
An kayyade adadin masu kai masa ziyasa
"Ba zai iya fita daga gidansa ba sai da izinin shugaban 'yan sandan Saliyo, in ji Bah a sakon da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a baya ake kira Twitter.
Bah ya kara da cewa daga yanzu za a bar mutum uku ne kadai su ziyarci Koroma daga iyalansa da kuma jami'an jam'iyyarsa -- kuma sai shugaban 'yan sanda ya amince kafin su gana ranar Litinin.
A sanarwar da ofishin Koroma ya fitar, daya daga cikin lauyoyinsa ya musanta cewa ana yi masa daurin-talala sai dai ya ce "an kara yawan jami'an tsaro a kusa da gidansa da kuma titunan da ke hanyar gidan".
An kama gomman mutane
Ranar Alhamis din da ta gabata aka tura wa Koroma sammaci domin ya hallara a ofishin 'yan sanda da ke Freetown cikin awa 24, a wani bangare na bincike bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan jiya.
Da sanyin safiyar ranar 26 ga watan Nuwamba ne wasu dauke da makamai suka kai hari a rundunar soji da barikin soji biyu da gidajen yari biyu da manyan ofisoshin ‘yan sanda biyi, inda suka yi gumurzu da jami’an tsaro.
Lamarin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 21, a cewar Ministan Watsa Labarai na kasar Chernor Bah.
Tun daga lokacin an kama akalla mutum 71 bisa hannu a abin da Shugaba Bio ya bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki.