Hukumomi a Amurka sun kama wani ɗan Nijeriya bisa samunsa da laifin haɗa baki da damfara ta intanet da satar bayanan sirri da kuma hannu a satar kusan dala miliyan 10 na shirin tallafin Covid-19 ga ma'aikata a Amurka.
Ofishin mai shigar da ƙara na Amurka a jihar Massachusetts ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na intanet a ranar Litinin kan kama ɗan Nijeriya mai suna Yomi Jones Olayeye, wanda aka fi sani da Sabbiea.
An kama Olayeye, ɗan asalin jihar Lagos da ke kudu maso yammacin Nijeriya, a ranar 13 ga watan Augusta, a yayin da ya isa filin jiragen sama na John F. Kennedy da ke birnin New York, in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ''takardar ƙarar da aka shigar tsakanin watan Maris da Yulin 2020, ta bayyana cewa Olayeye da abokan aikinsa sun damfari shirye-shirye guda uku na tallafin Covid-19 na ma'aikata wanda Ma'aikatar Tallafa wa marasa aikin yi ta Massachusetts da sauran hukumomin inshorar tallafa wa marasa aikin yi da buƙatu na musamman a Amurka tare da tallafin shirin ba da tallafi na Covid-19 na UI da PUA da kuma Tallafin Tarayya na FPUC.''
Kazalika sanarwa ta ce ''Musamman, Olayeye tare da haɗin gwiwar abokan aikinsa sun yi amfani da bayanan sirri na (PII) da suka saya ta shafin masu aikata laifuka a intanet don samun damar yin rajistar mazauna na boge a jihar da annobar Covid 19 ta shafa don samun tallafin shirin UI da PUA da kuma FPUC.''
Haka kuma Olayeye da abokansa sun buɗe asusun ajiyar banki na Amurka da kuma asusun katin cire kuɗaɗen da suka sace ta hanyar amfani da bayanan sirrin shirye-shirye ba da tallafin Covid-19 na ma'aikatan ƙasar.
Daga nan ne suka yi amfani da da ƙudaden da suka samu wajen sayen Bitcoin ta kasuwannin intanet.
“Olayeye da abokansa sun damfari shirye-shiryen ba da tallafin a jihohin Massachusetts da Hawaii da Indiana da Michigan da Pennsylvania da Montana da Maine da Ohio da kuma Washington," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Dokar Amurka ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari da kuma biyan tara ta dala 250,000 ko ninkin hakan da maido da kadarorin da ake tuhumar wanda aka kama da laifin damfara ta intanet da haɗa baki ko zamba.
Sannan zargin satar bayanan sirri kuwa an tanadi ƙara hukuncin ɗaurin shekaru biyu a kan duk wani hukuncin da aka yanke kan laifin damfara da zamba.