Sai dai Shettima ya nuna damuwa kan matsalar kuɗi da wasu marasa lafiya ke fuskanta./Hoto: Kashim Shettima/Facebook

Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce Amurkawa 13 aka yi wa dashen ƙoda a ƙasar a yayin da ake samun ƙarin masu zuwa Nijeriyar don neman lafiya daga wasu ƙasashe.

Wata sanarwa da Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Watsa Labarai da Sadarwa, Stanley Nkwocha ya fitar, ta ce Kashim Shettima ya fadi haka ne a ranar Alhamis a yayin da Ƙungiyar Likitocin da Suka Ƙware a Ciwon Ƙoda suka ziyarce shi a Fadar Gwamnati.

Ƙungiyar likitocin ta ziyarce shi ne gabanin babban taronta na Kimiyya Karo na 37 da za ta yi daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Fabrairu a Abuja, mai taken “Kawo Sauyi a Fannin Ciwon Ƙoda a Nijeriya.”

Shettima ya ce ana samun ƙaruwar masu zuwa Nijeriya neman lafiya ne daga ƙasashe irin su Amurka da sauran su saboda ƙwarewar likitocin Nijeriya da sauƙin da ake samu a fannin kiwon lafiya a ƙasar idan aka kwatanta da waɗancan ƙasashen.

A don haka ne Mataimakin Shugaban Ƙasar ya jaddada buƙatar cigaba da zuba-jari a fannin ƙwarewar ilimin likitanci don wannan abu ya cigaba da kasancewa.

Ya ce, “An samu sauyi a wajen zuwa neman lafiya a baya bayan nan saboda irin kulawar da ake samu a wasu asibitocinmu. Kwanan baya majinyata 13 daga ƙasar Amurka sun zo Nijeriya domin yin dashen ƙoda a Cibiyar Zenith Medical and Kidney Centre saboda ya fi araha sosai a nan, kuma suna da ƙwarewa iri ɗaya da ake da ita a ko ina a duniya.”

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yaba wa Dr. Olalekan Olatise, babban daraktan kula da lafiya na cibiyar Zenith bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen kula da ƙoda, inda ya bayyana shi a matsayin “mutum mai mutunci da kishin ƙasa” a ƙoƙarinsa na taimakon bil’adama.

Sai dai Shettima ya nuna damuwa kan matsalar kuɗi da wasu marasa lafiya ke fuskanta, wadanda da yawa daga cikinsu suke sayar da gidajensu ko kuma suke dogaro da tallafin gwamnati don samun yin dashen ƙodar.

“Yayin da yin dashen ƙoda babban ƙalubale ne, rayuwa bayan dashen na haifar da ƙarin matsaloli. Yawancin marasa lafiya suna kokawa kan tsadar kula da lafiya bayan yin dashen, gami da sayen magungunan rigakafi, waɗanda ke da muhimmanci don kiyaye lafiyarsu,” in ji shi.

Tuna baya

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya tuno da tsare-tsaren kiwon lafiya da ya fara a lokacin da yake gwamnan jihar Borno, da kuma nasarorin da ake samu a ci gaba da gudanar da shirye-shiryen kula da mata masu juna biyu kyauta da ya ɓullo da su.

“A wani asibiti da ke unguwarmu, muna ba da buhun shinkafa da na wake ga kowace sabuwar mai jego. Ana samun aƙalla mata 30 da ke haihuwa a kullum, fiye da wanda ake samu a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri (UMTH).

Bayan da aka tattara sun nuna an haihu sau 4,000 a cikin kasa da watanni takwas, tare da biya musu dukkan kudaden jinya, ciki har da na wadanda aka yi wa tiyata,” in ji Shettima.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma nanata bukatar Nijeriya ta samar da kuma inganta ma’aikatanta na kiwon lafiya, inda ya ce a lokacin da yake gwamnan jihar Borno ya tura ɗalibai mata 60 domin karatun likitanci a kasar Sudan.

"Dole ne mu kashe kuɗaɗe a fannin ilimin kiwon lafiya na musamman a wannan ƙasa," in ji Shettima.

Kungiyar Likitocin Ƙodar ta ce a wajen babban taron nata, za ta karrama Mataimakin Shugaban Kasa da Lambar Yabo ta Gwarzon Koda kokarinsa na bayar da tallafi ga majinyatan ƙoda da kuma bayar da shawarar kafa dakin gwaje-gwaje na musamman don kula da dashen dashe.

TRT Afrika