A ranar 24 ga watan Maris ake sa ran gudanar da babban zaɓe a ƙasar. / Hoto: Reuters

Ƴan takarar shugaban ƙasa a Senegal sun ƙaddamar da gajeren yaƙin neman zaɓensu a ranar Asabar, kwana biyu bayan kotu ta tabbatar da cewa za a gudanar da zaɓen ƙasar a ranar 24 ga watan Maris, wanda hakan ya kawo ƙarshen zaman rashin tabbas da ake ciki kan zaɓen ƙasar.

An kasance cikin zaman fargaba a ƙasar tun farkon watan Fabrairu bayan shugaban ƙasar Macky Sall ya ɗaga zaɓen ƙasar da watanni goma wanda tun farko aka yi niyyar gudanarwa 25 ga watan Fabrairu, lamarin da ya jawo zanga-zanga a ƙasar wadda har ta rikiɗe ta zama tarzoma.

Senegal wadda ƙasa ce mai mutum miliyan 18, ta kasance ƙasar da ke da kyakkyawar dimoƙuradiyya a Yammacin Afirka.

Sai dai rikicin kan batun gudanar da zaɓe a ƙasar ya soma zuwa ƙarshe ne tun bayan da Kotun Tsarin Mulki ta ƙasar ta yanke hukunci kan cewa dole ne a gudanar da zaɓe kafin wa’adin Sall ya kawo ƙarshe a ranar 2 ga watan Afrilu.

Sakamakon sabon lokacin da aka saka kan zaɓen, ƴan takara 19 na shugabancin ƙasar na da ƙasa da ƙasa da mako uku su nemi goyon bayan jama’a.

Wannan na nufin kuma a karon farko, za a gudanar da yaƙin neman zaɓe a cikin watan Ramadana a ƙasar wadda Musulmai ne suka fi rinjaye a cikinta.

“Dole ne mu saba da komai,” kamar yadda ɗan takara daga jam’iyyar adawa kuma tsohon magajin garin Dakar, Khalifa Sall ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

“Mun saba da manyan bukukuwa, sai dai wannan bikin bai dace da watan Ramadana ba, wanda lokaci ne na tuba da sada zumunta.”

Haka kuma lokacin yaƙin neman zaɓen ya zo daidai da lokacin da Kiristoci ke nasu azumin.

Reuters