Facebook da Instagram da kuma WhatApp suna daga cikin kafofin da aka taƙaita amfani da su a Mozamboque. / Hoto: Reuters

An takaita amfani da kafofin soshiyal midiya a Mozambique karo na biyu cikin mako guda a ranar Alhamis, a cewar wani shafin da ke sa ido kan kafofin intanet.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan adawa ke kira kan a shiga yin yajin-aiki a faɗin ƙasar, saboda taƙaddamar da ta ɓarke a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.

Hatsaniya ta ɓarke a ƙasar da ke yankin kudancin Afirka, bayan da jam'iyyar Frelimo wadda ta shafe shekaru 49 tana mulki ta sake lashe zaɓen da aka gudanar a 9 ga Oktoba, wanda jam'iyyun adawa da masu sa-ido kan zaɓen suka ce yana cike da kurakurai.

"Za mu iya tabbatar da cewa an taƙaita amfani da kafofin soshiyal midiya a Mozambique,'' a cewar shafin NetBlocks wanda babban ofishinsa yake birnin Landan, yana mai ƙari da cewa Facebook da Intsagram da WhatsApp suna daga cikin kafofin da aka taƙaita amfani da su.

A ranar Juma’ar da ta wuce ne aka katse hanyoyin amfani da kafofin, kuma kwana guda bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon zaɓen da aka gudanar da jami'an tsaro suka tilasta hana gudanar da zanga-zanga.

'Katse hanyoyin Intanet'

NetBlocks ya ce a lokacin ''kusan an katse dukka hanyoyin Intanet na wayoyin hannu a Mozambique.''

A ranar 24 ga watan Oktoba aka ayyana Daniel Chapo na jam'iyyar Frelimo, mai shekaru 47, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da kusan kashi 71 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Shugaban 'yan adawa Venancio Mondlane, mai shekaru 50, daga ƙaramar jam'iyya ta Podemos ya zo na biyu da kashi 20 cikin 100.

Bayan sanarwar, 'yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar magoya bayan ɗan adawan da suka fito kan tituna.

Munanan zanga-zanga

Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch (HRW) ta ce aƙalla mutane 11 ne jami'an tsaro suka kashe, tare da jikkata fiye da mutum 50 a ranakun 24 da 25 ga Oktoba.

Sai dai ‘yan sanda ba su mayar da martani kan rahoton na HRW ba, amma a baya sun ce mutane 20 ne suka jikkata a hatsaniyar da ta biyo bayan zaɓen, kana mutum biyu sun mutu ba tare da wani ƙarin bayani ba.

'Yan sanda sun ƙaddamar da bincike kan Venancio Mondlane, bayan rikicin, sai dai har yanzu ba a san inda yake ba.

Tsohon ɗan jaridan wanda ya koma ɗan siyasa kana yake amfani da kafofin soshiyal midiya wajen yaɗa manufarsa ga magoya bayansa, ya yi kira da a gudanar da zanga-zanga, kuma a shiga yajin aikin na gama-gari daga ranar 31 ga Oktoba zuwa 7 ga Nuwamba.

Birnin ya zama tamkar maƙabarta

Babu tabbas ko za a amsa kiransa na ''gudanar da yajin-aiki'' tun daga arewacin Cabo Delgabo zuwa Maputo da ke da nisan kilomita sama da 2,400 (kimanin mil 1,500). Sai dai babban birnin ƙasar ya kasance tamkar makabarta a ranar Alhamis.

'Yan sanda sun aika saƙonni ta wayoyi a ranar Laraba da safiyar Alhamis, wanda wani ɗan jaridan AFP ya tabbatar da samun saƙon da ya umarci mazauna yankin da ka da su shiga cikin kowane aikin da ka iya jefa ƙasar cikin ''ruɗani.''

Kurakuran zaɓe

Shugaban jam'iyyar Podemos, Albino Forquilha ya fada a ranar Alhamis cewa, "Zai yi dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da cewa ba a samu tashin hankali ba yayin yajin-aikin na tsawon mako guda, "amma muna buƙatar yin gwagwarmaya don tabbatar da adalci".

Masu sa-ido kan harkokin zaɓen, ciki har da ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), sun bayyana samun manyan kurakurai kafin, da yayin, da kuma bayan zaɓen.

A ranar Lahadi da ta gabata ne Mondlane da jam'iyyarsa ta Podemos, wadda ta sha gaban babbar jam'iyyar adawa ta Renamo a zaben, suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun tsarin mulkin ƙasar domin a sake ƙidayar ƙuri'u.

Tuni dai kotun ta buƙaci hukumar zaɓen ta gabatar mata da takardar sakamakon zaɓen, da kuma lokuta na rumfunan zaɓe a larduna shida har da na Maputo, inda ta ba su kwanaki takwas don gabatar da takardun.

AFP