Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya (NCAA) ta bayyana damuwarta a kan yadda ake samun yawan soke tashin jirage a cikin ƙasar a baya bayan nan.
Shugaban hukumar, Kyaftin Chris Najomo ya bayyana cewa daga cikin jirage 5,291 da suke yi aiki a watan Satumban 2024, an jinkirta tashin 2,434, yayin da aka soke tashin 79.
Ya ƙara da cewa daga cikin jirage 5,513 da suka yi aiki a watan Oktoban 2024 kuma, an jinkirta tashin 2791, yayin da aka soke tashin 111.
Najomo ya fadin hakan ne a ranar Juma’a a lokacin wani taron masu ruwan da tsaki mai taken “Gano sahihiyar mafita ga rusa tsarin zirga-zirgar jiragen sama.”
Waɗanda suka halarci taron sun hada da Shugabar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAAN), Mrs. Olubunmi Kuku, da wakilan Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Nijeriya NAMA, da kuma na Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NIMET), da sauran su, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Shugaban hukumar NCAA ya ce ana ta kiransa daga Fadar Shugaban Ƙasa da Majalisar Dokoki da kuma ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Ya ce “Shugaban Majalisar Dattijai ya kira ni yana tambayar me muke yi a kan wannan matsala. Abubuwa da dama sun faru a cikin mako dayan da ya wuce.
Sai dai shugaban NCAA din ya ce duk da ya fahimci matsalolin da kamfanonin jiragen sama ke fuskanta to fa ba zai zuba ido a ci gaba da wannan tsari ba tare da daukar mataki ba.
Ya kara da cewa "Samun jinkiri da soke tashin jirage da ake yawan samu suna rushe tsare-tsare, suna haifar da asarar kudi da kuma raunana amincewar masana'antu," in ji shi.
Sannan ya tunatar da kamfanonin jiragen sama kan dokokin hukumar NCAA na batun sokewa da jinkirar tashin jirage.
“Wadannan dokokin amfani da su ba zabi ba ne, tilas ne, domin tabbatar da cewa an sanar da fasinjoji duk wani sauyi na tashin jirage ko sokewa a kan lokaci, tare da biyansu duk abin d aya shafi masauki da abinci sakamakon sokewar,” in ji shi.
Najomo ya kuma shawarci kamfanonin jiragen saman da su dinga nuna ƙwarewa wajen mu’amala da fasinjoji kan abin da ya shafi jinkirin tashin jirage ko sokewa.
Sai kuma ya gargadi fasinjoji da su guji lalata kayayyakin filayen jirgi ko dukan ma’aikata a yayin nuna fushi kan irin wannan matsala.