An soke tafiyar Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima zuwa ƙasar Samoa inda zai wakilci Nijeriya a taron shugabannin ƙasashen rainon Ingila.
An soke tafiyar ne bayan wani abu ya faɗa kan jirgin na Shettima a yayin da ya yada zango a filin jirgin JFK da ke birnin New York na Amurka.
A wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Nijeriya Bayo Onanuga ya fitar, wani abu da ya faɗa kan jirgin ya lalata gilas ɗin direban jirgin.
Sanarwar ta ƙara da cewa tuni Shugaba Tinubu ya amince da wata tawagar ministoci wadda za ta wakilci Nijeriyar a Apia babban birnin Samoa kafin a kammala gyaran jirgin.
Ministan Muhalli na Nijeriya Balarabe Abbas Lawal shi ne zai jagoranci tawagar da za ta wakilci Nijeriya a taron na ƙasashen rainon Ingila.
An soma taron ne tun a ranar 21 ga watan Oktoba inda za a kammala shi a ranar 26 ga Oktoba.
Tuni dai Mataimakin Shugaban Nijeriyar Kashim Shettima da ministan harkokin waje Yusuf Tuggar sun bar birnin New York zuwa Najeriya bayan faruwar wannan lamarin.