Rahoton ya ce "kwararar da 'yan ta'adda suke yi (zuwa Kano) ta faru ne sakamakon farmakin da sojoji ke kai wa 'yan bindiga da abokan aikinsu a jihohi irin su Katsina, Sokoto da Zamfara."/Hoto: Reuters

Jami'an tsaro a Kano, birni mafi girma a arewacin Nijeriya suna cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon wasu rahotanni na kwararar 'yan bindiga daga jihohi maƙota inda sojojin ƙasar ke kai musu farmaki.

'Yan bindiga da ke garkuwa da mutane sun kwashe tsawon shekaru suna aikata muggan laifuka a jihohin arewa maso-yamma da arewa ta tsakiyar Nijeriya, inda suke kai hare-hare a ƙauyuka tare da kashewa da garkuwa da mutane, da ma ƙona garuruwan.

Ɓata-garin na da manyan sansanoni a dazukan Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja, kuma suna garkuwa da mutanen da suka haɗa da ɗaliban makarantu.

Wani rahoto na bayanan sirri da aka aika zuwa ga ofishin gwamnan Kano daga fadar gwamnatin jihar Zamfara a ranar Litinin ya yi gargaɗin cewar 'yan bindiga daga Zamfara na tserewa zuwa Kano don samun mafaka.

Rahoton ya jero irin barazanar da 'yan bindiga suke yi a yayin da suke barin yankunan da suke, zuwa birnin na Kano mai miliyoyin mutane.

Kano na da nisa daga matattarar rikicin, kuma yaɗuwar ta'addanci zuwa yankin da yake cibiyar kasuwanci na sanya damuwa a zukatan mahukunta.

Farmakin sojoji na korar 'yan ta'adda

Rahoton na ɗauke da sa hannun Bashir Makama, mataimakin sufuritandan 'yan sanda da ke aiki da Sashen Bayanan Sirri na ofishin Gwamnan Jihar Zamfara, wanda aka kuma miƙa wa hukumomin tsaro a Kano.

Rahoton ya ce "kwararar da 'yan ta'adda suke yi (zuwa Kano) ta faru ne sakamakon farmakin da sojoji ke kai wa 'yan bindiga da abokan aikinsu a jihohi irin su Katsina, Sokoto da Zamfara."

A 'yan makonnin nan sojojin Nijeriya sun ƙaddamar da farmaki kan 'yan bindiga a Zamfara da Sokoto da zummar murƙushe su.

Hare-haren sojojin sun kashe 'yan ta'adda da dama da suka haɗa da shugabanninsu irin su Halilu Sububu, wanda shi ne shugaban 'yan bindiga a arewa maso-yammacin Nijeriya.

Sayen gidaje ga 'yan bindiga

Rahoton ya ci gaba da cewa abokan aikin 'yan bindigar na zuwa Kano tare da sayen gidaje da za a yi amfani da su a matsayin mafaka ga 'yan ta'addar da ma iyalansu.

Rahoton bai bayyana adadin 'yan bindigar da ya zuwa yanzu suka gudu zuwa Kano ba, amma ya bayyana wasu yankuna shida da suka fi sayen gidaje.

Rahoton ya buƙaci jami'an 'yan sanda da su sanya idanu kan dillalai da gidajen da mutanen Sokoto da Zamfarake suke saya.

"Mun samu saƙo daga jihar Zamfara"

Jami'an tsaro a Kano sun bayyana cewar sun samu bayanan sirri kan tsaro daga jihar Zamfara.

"Mun riga mun sani cewa 'yan ta'adda da 'yan bindiga na shigowa wasu yankunan Kano, kuma muna aiki don daƙile barazanar," a cewar wani jami'in tsaro a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP.

"Muna aiki cikin sirri don ganin jama'a ba su tayar da hankali a garin ba," in ji majiyar.

Jam'an tsaron na Kano sun kuma bayyana cewar ba su yi ƙasa a gwiwa ba tun 2009 a lokacin da 'yan ta'addar Boko Haram suka shiga Kano daga Maiduguri.

"Waɗannan bayanan sirri daga Zamfara tunatarwa ce ta kar mu yi ƙasa a gwiwa," in ji wani jami'in tsaron na daban da shi ma ya nemi a ɓoye sunansa.

Kano na jan hankalin mutane baƙi daga yankin da ma sassan Nijeriya daban-daban.

TRT Afrika da abokan hulda