Ƴan sandan Zimbabwe sun ceto yara 251 da gano kaburbura a wurin ibadar wani mai da'awar Annabta

Ƴan sandan Zimbabwe sun ceto yara 251 da gano kaburbura a wurin ibadar wani mai da'awar Annabta

Ƴan sandan sun ce daga cikin kaburburan da suka gano akwai na jarirai bakwai wadanda hukumomi ba su yi rajistar binne su ba.
 Ƴan sandan Zimbabwe sun ce suna kan gudanar da bincike kan gano kaburburan. Hoto: AFP  

Ƴan sandan kasar Zimbabwe sun sanar da kama wani mutum da ake zargi yana da'awar shi Annabi ne ga mabiyansa na darikar katolika a ranar Laraba.

An yi kamen ne a wani wurin ibada inda wadanda suka yi imani ke zama, kuma hukumomi sun gano wasu kaburbura 16 da ba a yi musu rajista ba, ciki har da na jarirai, da kuma yara sama da 250 da ake amfani da su don aikatau.

A cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan Paul Nyathi ya fitar, ya ce Ismael Chokurongerwa mai shekara 56, wanda ke ikirarin shi Annabi ne, yana jagorantar wata ƙungiya da ke da mambobi sama da 1,000 a wata gona mai tazarar kilomita 34 daga arewa maso yammacin babban birnin kasar, Harare, inda yaran suke zaune tare da sauran mutanen da suka yi imani da shi.

Ya ce "ana amfani da yaran don yi wa ƙungiyar hidima ta hanyar aikatau," in ji shi. Daga cikin yaran 251, an gano 246 ba su da takardar shaidar haihuwa.

"Ƴan sanda sun tabbatar da cewa dukka yaran sun kai shekarun zuwa makaranta amma baki daya ba sa zuwa kuma ana cin zarafinsu ta hanyar bautar da su da ayyukan hannu daban-daban da sunan ana koya musu dabarun rayuwa," in ji Nyathi.

'Laifuka'

Ƴan sandan sun ce daga cikin kaburburan da suka gano akwai na jarirai bakwai wadanda hukumomi ba su yi rajistar binne su ba.

Ya ce jami’an ƴan sanda sun kai samame wurin ibadar a ranar Talata. An kama Chokurongerwa, wanda yake kiran kansa da Annabi Ishmael tare da wasu mataimakansa guda bakwai "kan aikata wasu laifuffuka da suka haɗa da cin zarafin ƙananan yara."

Nyathi ya ce nan gaba za a fitar da ƙarin bayanai "a kan lokaci yayin da bincike ke ci gaba da gudana."

Wata jarida ta gwamnati mai suna H-Metro da ta raka ƴan sandan a yayin farmakin da suka kai wurin ibadar, ta nuna yanda ƴan sanda sanye da kayan kwantar da tarzoma suna jayayya da wasu mata da suka yi imani sanye da fararen kaya da hular rufe kai wadanda suka buƙaci a dawo da yaran da aka saka a cikin motar jami'an da ke jira.

Ba a dai bayyana inda ƴan sandan suka kai yaran da wasu mata da suka raka su ba.

'Rashin ilimin Boko'

“Me yasa suke daukar yaranmu? Muna jin dadinmu a nan. Ba mu da wata matsala a nan,” in ji daya daga cikin matan a cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin jaridar na X, wanda aka fi sanin da Twitter a baya.

A cewar jaridar, jami'an 'yan sanda dauke da bindigogi da hayaƙi mai sa hawaye da kuma karnuka da aka horar sun "gudanar da wani gagarumin farmaki" a wurin ibadar. Mabiyan sun bayyana wurin ibadar tasu a matsayin "ƙasar alkawarinsu."

Daya daga cikin mataimakan Chokurongerwa ya yi hira da jaridar.

“Imaninmu ba daga nassosi ba ne, muna samo shi ne kai tsaye daga Allah wanda ya ba mu dokoki kan yadda za mu shiga aljanna.

"Allah ya haramta karatun boko saboda darasin da ake koyarwa a irin wadannan makarantu ya saɓa wa ƙa’idarsa,” in ji shi.

Kazalika ya ƙara da cewa “Allah ya shaida mana ba za a yi ruwan sama ba idan muka tura yaranmu makaranta. Dubi yanda ake fama da matsalar fari a can, amma duk da haka mu muna samun ruwan sama a nan. Muna da baiwar kunnuwan sauraren muryar Allah,'' a cewar mutumin.

'Azabtarwa zuwa ga mutuwa'

Ƙungiyoyin darikar katolika waɗanda ke cusa ra'ayin gargajiya cikin koyarwarsu ta mazahabar Pentikostal sun shahara a ƙasar Afirka ta kudu mai zurfi a addini.

Ana da karancin bincike kan majami'un katolika a Zimbabwe, amma wani bincike da Asusun kula da Ƙananan yara na Majalisar Dikin Duniya UNICEF ya kiyasta cewa ita ce babbar mazhabar addini da ke da mabiya kusan miliyan 2.5 a ƙasar mai al'umma miliyan 15.

Wasu daga cikin kungiyoyin suna bin koyarwar da ta bukaci mabiya su guji karatun boko ga ’ya’yansu da kuma magunguna da kula da lafiya ga mambobin wadanda a maimakon haka dole su nemi waraka ta hanyar yin imani da kuma addu’o'i da ruwa mai tsarki.

A shekarun baya-bayan nan, wasu sun fara bai wa mambobinsu damar ziyartar asibitoci da sanya yara a makaranta sakamakon irin yakin neman zabe da gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu suke yi.

A watan Afrilun shekarar da ta gabata, ƴan sanda a Kenya sun kama wani Fasto da ake zargin ya umurci mabiyansa su azabtar da kansu da yunwa don su samu damar gana wa da Yesu Almasihu.

A watan Janairu ne babban mai shigar da ƙara na ƙasar ya ba da umarnin a tuhumi faston, Paul Mackenzie, da kuma mutum sama da 90 daga kungiyar asirin, da laifin kisa da zalunci da azabtar da yara da sauran laifuffuka da suka shafi mutuwar mutum 429 da ake kyautata zaton mambobin cocin ne.

TRT Afrika