A dokar ƙasar Ghana, ana aurar da mutum ne idan ya kai shekara 18./Hoto: Rundunar Ƴan sandan Ghana

Rundunar ƴan sandan ƙasar Ghana ta ce ta karɓo wata yarinya ƴar shekara goma sha biyu da ake zargi wani malamin cocin gargajiya mai ƙarfin faɗa-a-ji ya aura a ƙarshen makon jiya.

Wata sanarwar da rundunar ta fitar ranar Talata da asuba ta ce yarinyar, wadda ake zargi Gborbu Wulomo, Nuumo Borketey Laweh Tsuru XXXIII ya aura, tana hannunsu ita da mahaifiyarta.

"Rundunar ƴan sandan Ghana ta gano yarinyar ƴar shekara 12 da ake zargi an aurar da ita ga Gborbu Wulomo, mai shekara 63 a yankin Nungua na birnin Accra. Yanzu haka yarinyar da mahaifiyarta suna ƙarƙashin kulawar ƴan sanda," in ji sanarwar.

Rundunar ta ƙara da cewa tana aiki da Ma'aikatar Kula da Iyali da Ƙananan Yara da Walwala ta Ghana domin bai wa yarinyar "taimakon da ya kamata" a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Kakkausar suka

Ƴan ƙasar Ghana, musamman masu mua'ala da shafukan sada zumunta, sun yi ta kakkausar suka bayan da wani bidiyo da ya nuna yadda ake ɗaura auren Gborbu Wulomo da yarinyar ƴar shekara 12.

A dokar ƙasar Ghana, ana aurar da mutum ne idan ya kai shekara 18.

Sai dai wata ƙungiya mai zamanta mai suna Girls Not Brides, ta ce ana aurar da kashi 19 na ƙananan yara mata a Ghana kafin su kai shekara 18 yayin da ake aurar da kashi 5 kafin su kai shekara 15.

TRT Afrika