Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo Felix Tshisekedi ya sake lashe zaben kasar, kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana a ranar Lahadi.
Hukumar zaben kasar CENI ta ce Tshisekedi ya samu kashi 73.34 cikin 100 na kuri'un kasar da aka jefa a zaben da 'yan takara 20 suka fafata, daga ciki har da shahararren mai hakar ma'adinan nan Moise Katumbi da dan adawar nan Martin Fayulu.
Katumbi da Fayulu su suka zo na biyu da na uku bayan an ba su tazara mai yawa a zaben da aka gudanar a ranar 20 ga watan Disamba.
Kamar yadda CENI ta bayyana, wanda ya zo na biyu wato Katumbi ya samu kaso 18 cikin 100 na kuri'un da aka jefa.
'Yan adawa a kasar a ranar Lahadi sun yi kira da a fito zanga-zanga bayan Tshisekedi mai shekara 60 an ayyana shi a matayin wanda ya lashe zaben kasar.
'Magudin zabe'
Katumbi da Fayulu wadanda su ne wadanda suka zo na biyu da na uku sun zargi CENI da goyon bayan Tshisekedi a zaben kasar wanda ya hau kan karagar mulki a Janairun 2019 bayan ya ci zaben da aka gudanar 30 ga watan Disamba.
Tshisekedi na fuskantar kalubalen tabbatar da tsaro a gabashin kasar mai fama da rikici, da kawar da talauci da kuma hada kan kasar bayan zaben kasar da aka gudanar wanda ya raba kan kasar.
Sama da mutum miliyan 40 suke da rajistar zabe a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sai dai mutane kalilan ne suka fito zaben, kamar yadda sakamakon zaben da CENI ta fitar ya tabbatar.