Hauwawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta karu da kaso 0.38 a cikin wata guda.
Hukumar kididdiga ta Nijeriya NBC ta ruwaito cewa a watan Mayu hauhawar farashin na kan maki 22.41 inda a watan Yuni ya karu zuwa 22.79 a ranar Litinin.
Hakan na nufin an samu karuwa da kashi 4.19 cikin 100 cikin shekara guda idan aka kwatanta da Yunin 2022 wanda hauhawar farashin ke kan kashi 18.60.
A makon da ya gabata gwamnatin Nijeriya ta saka dokar ta-baci kan abinci sakamakon karuwar kudin abinci.
An yi ta samun hauhawar farashi a Nijeriya tun daga 2016, lamarin da ya sa Babban Bankin Kasar ya yi ta kara farashin ruwa na karbar bashi.
Hauhawar farashin da aka samu a wannan karon shi ne mafi yawa a tsawon shekaru
TRT Afrika