An saki dubban fursunoni daga gidajen yari daban-daban a Nijeria a yunkurin gwamnatin kasar na rage cunkoso a gidajen, kamar yadda Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana a shafinsa na sada zumunta a karshen mako.
Wannan yana cikin kudurin shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, wanda aka zabe shi a farkon shekarar nan, na rage cunkoson gidajen kaso, a cewar ministan.
"Jiya sun soma sakin fursunoni 4,068 cikin 80,804 da ke gidajen gyaran hali 253 a fadin kasar nan, wadanda ake tsare da su saboda sun gaza biyan tarar da aka sanya musu," in ji Olubunmi Tunji-Ojo a sakon da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a baya ake kira Twitter.
Ya sanar da daukar matakin ne bayan ya kai ziyara gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin kasar.
Kakakin ministan Ajibola Afonja ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "fursunonin da tarar da aka sanya musu ba ta wuce ta naira miliyan daya ba ne kadai za su ci moriyar wannan shiri."
Afonja ya kara da cewa sun soke tarar da ta kai naira miliyan 585 da aka sanya wa wasu fursunoni.
Tinubu ya yi alkawarin daukar sabbin matakai na rage yawan fursunoni a gidajen yari, yana mai cewa za a rika hukunta masu laifi ta wasu hanyoyin ba tare da an garkame su ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin fursunonin da ke gidajen yarin Nijeriya ya zarta kashi 147 na wadanda ya kamata su kasance a ciki kuma mutanen da aka tsare kan kwashe shekaru ba tare da an kammala shari'arsu ba.