Sakin nasa zai iya yin tasiri sosai a zaɓen shugaban ƙasar, domin kuwa Sonko yana da ɗimbin magoya baya musamman matasa. Hoto: AFP

An saki babban ɗan adawa na Senegal Ousmane Sonko da mutumin da yake mara wa baya a takarar shugaban ƙasa Bassirou Diomaye Faye daga gidan yarin Dakar kwanaki 10 kafin gudanar da babban zaɓen ƙasar.

"A kan idanunmu suna fito daga kurkuku," a cewarsa lauyansa Cheikh Koureyssi Ba ranar Alhamis da daddare, a yayin da wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya ga lokacin da jerin gwanon motocinsa suka fita daga gidan yari inda mutane suke ta yi masa jinjina.

An saki Sonko ne bayan an kwashe makonni ana gudanar da zanga-zanga a Senegal sakamakon matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na ɗage zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kazalika sakin nasu na zuwa ne bayan majalisar dokokin ƙasar ta amince da wani ƙuduri ranar 6 ga watan Maris wanda ya yi afuwa ga ƴan adawa aka ɗaure a yayin da hukumomin ƙasar suke neman kwantar da hankulan jama'a sakamakon ɗage zaɓen da Shugaba Macky Sall ya yi.

Sakin nasa zai iya yin tasiri sosai a zaɓen shugaban ƙasar, domin kuwa Sonko yana da ɗimbin magoya baya musamman matasa.

A watan Yulin da ya gabata ne aka ɗaure Sonko a kurkuku bayan an zarge shi da " fyaɗe da gurɓata tarbiyyar matasa" - zargin da ya musanta kuma ya ce yana da alaƙa da siyasa.

Shi ne ɗan takara na uku mafi yawan ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar na 2019 sai dai an hana shi tsayawa takara a zaɓen da za a yi a 2024. Kazalika an rusa jam'iyyarsa.

Daga nan ne Sonko ya mara wa Faye baya a zaɓen da ke tafe, wanda tun a watan Afrilun 2023 yake ɗaure a kurkuku.

TRT Afrika da abokan hulda