Hukumar da ke lura da sufurin jiragen sama a Sudan ta sake tsawaita wa'adin bude filiyen jiragen saman kasar zuwa 15 ga watan Agusta.
Hukumar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ranar Litinin da sanyin safiya.
Sai dai ta ce za ta ci gaba da bayar da dama ga jiragen da ke kwashe mutane daga kasar da kuma wadanda ke kai agaji su sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Khartoum.
Ranar 9 ga watan Yuli ne hukumar kula da sufurin jiragen sama a Sudan ta ce ta tsawaita rufe sararin samaniyar kasar zuwa ranar 31 ga watan Yuli.
Hakan na faruwa ne a yayin da ake ci gaba da fafatawa tsakanin sojojin kasar da dakarun runduna ta musamman ta Rapid Support Forces (RSF) wadda aka soma tun tsakiyar watan Afrilu.
Bayanai daga kungiyoyin bayar da agaji da masu aikin sa-kai na cewa yakin ya yi sanadin mutuwar tsakanin mutum 3000 zuwa 10000.
Sai dai Ma'aikatar Lafiya ta Sudan ta ce ya zuwa 5 ga watan Yuli, mutum 1,136 ne suka mutu sanadin yakin.
A karshen makon jiya, shugaban RSF Janar Mohamed Hamdan Dagalo, da ake kira Hemedti, ya yi kira a sauya shugabanci rundunar sojin kasar wadda mutumin da ke hamayya da shi Janar Abdel Fattah al-Burhan yake jagoranta.
Ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ya fitar a karon farko tun bayan barkewar yakin.
Hemedti ya nemi afuwar 'yan kasar Sudan bisa yadda yakin yake tasiri a rayuwarsu yana mai cewa “mun gaya wa 'yan uwanmu da ke rundunar soji cewa idan suna so a yi gaggawar samun mafita … ku sauya shugabancinku sannan za mu kulla yarjejeniya cikin awa 72.”
A gefe guda, Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa an kama hanyar mantawa da yakin Sudan duk da cewa akwai yara miliyan 14 da ke bukatar agaji.
"Akwai akalla yaran Sudan miliyan 14 da suke bukatar taimako. Hakan yana nufin daya cikin kowane yara biyu da ke Sudan," a cewar Ted Chaiban, Mataimakin Darakta a UNICEF kan Ayyukan JinKai a Sudan.