Tun da safiyar Lahadi aka soma jin karar harbe-harben bindiga. / Hoto: Julius Maada Bio

Kasar Saliyo ta saka dokar hana fita bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari barikin soji da kuma yunkurin afkawa sashen ajiye makamai na barikin a Freetown babban birnin kasar.

A wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar, ta bayyana cewa tuni jami’an tsaro suka shawo kan lamarin.

Tun da farko kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa ana ta jin karar harbe-harbe ba kakkautawa a cikin birnin na Freetown.

“Da safiyar Lahadi, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi yunkurin afakawa cikin ma’ajiyar makamai da ke barikin Wilberforce. An dakile su,” kamar yadda Ministan Watsa Labarai Chernor Bah ya bayyana a wata sanarwa.

“An saka dokar hana fita a kasa baki daya wadda za ta fara aiki nan take. Muna bayar da shawara da babbar murya kan ‘yan kasa su zauna a cikin gida,” in ji sanarwar.

Kare Dimokuradiyya

Shugaba Julius Maada Bio ya jinjina wa jami'an tsaro kan dakile harin da suka yi inda ya ce sun nuna jajircewa.

"Za mu ci gaba da jajircewa wajen ganin mun kare dimokuradiyya a Saliyo, kuma ina kira ga daukacin al'ummar Saliyo da su hada kai domin sauke nauyin da ke kanmu baki daya," kamar yadda ya wallafa a shafin X.

"Babu abin da ya kai zaman lafiyar kasarmu kuma za mu ci gaba da kiyaye kasarmu da samar da zaman lafiya a Saliyo da kuma yaki da duk wasu da ke son yi wa zaman lafiyarmu zagon-kasa," kamar yadda shugaban ya kara da cewa.

TRT Afrika