'Yan bindiga sun sace wasu daliban Jami'ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina a arewacin Nijeriya, kamar yadda ma magana da yawun jami'ar Malam Habibu Umar ya tabbatar wa TRT Afrika.
Jami'in ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da safe a gidajen da dalibai ke zama a wajen makarantar.
"Ba dakunan kwanan dalibai da ke cikin makaranta maharan suka shiga ba, a rukunin gidaje masu zaman kansu da dalibai ke kama haya ne 'yan bindigar suka je suka sace daliban," in ji Malam Habibu.
Amma ya ce a yanzu hukumar makaranta ba za ta iya tabbatar da yawan daliban da aka sace ko jinsinsu ba har sai ta kammala binciken da take yi.
Wannan ne karo na biyu da aka sace dalibai a makaranta a cikin kasa da mako biyu a Nijeriya, inda kwanan nan aka sace wasu daliban mata a Jami'ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara.
Sannan a ranar Litinin ma 'yan bindiga sun shiga Jami'ar Usman Danfodio ta Sokoto amma Allah Ya takaita ba su sace kowa ba sai kayan abinci.