Masu garkuwa da mutane sun sace mutum 19 a karamar hukumar Bwari, yayin da wasu mutum 30 kuma suka mutu sakamakon zaftarewar kasa lokacin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Kuje, duka a Abuja, babbar birnin tarayyar Nijeriya.
Shugabannin kananan hukumomin Bwari da Kuje John Gabaya da Abdullahi Sabo ne suka bayyana haka yayin da suke ganawa da Sabon Ministan Babban Birnin Tarayyar Abuja Nyesom Wike a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito.
Yayin da yake magana kan kalubalen da ke fuskantar yankinsa, Shugaban Karamar Hukumar Bwari John Gabaya ya ce "an sace mutum 19 a ranar Laraba a karamar hukumar Bwari."
Shugaban Karamar Hukumar Kuje Abdullahi Sabo shi kuwa ya yi korafi ne dangane da aikace-aikacen masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a yankinsa, inda ya ce "akwai mutum 30 da suka mutu bayan zaftarewar kasa a wurin da suke aikin hakar ma'adanai."
Yayin da yake mayar da martani kan matsalolin da shugabannin kananan hukumomin suka gabatar masa, Minista Wike ya yi alkawarin magancesu, inda ya ce a matsayinsa na tsohon shugaban karamar hukuma ya fahimci halin da suke ciki.
"Kalubalen tsaro babbar matsala ce a ko'ina, sannan ku da kuke zaune a wajen birnin Abuja, ya kamata ku yi aiki tukuru, kuma samar da bayanai abu ne mai muhimmanci sosai," in ji sabon ministan.
A karshe, Ministan ya bukaci duka shugabannin kananan hukumomi shida da ke birnin da su kafa rundunar sanya ido kan aikace-aikacen hakar ma'adanai a yankunansu.
Kazalika ya yi alkawarin ganawa da takwaransa Ministan Ma'adanai Dele Alake don kawo karshen aikace-aikacen hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a Babban Birnin na Nijeriya.