A ranar Laraba ne aka rantsar da sabon zababben shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a hukumance a karo na biyu.
Alƙalin Alƙalan Afirka ta Kudu Raymond Zondo ne ya rantsar da shi a wani gagarumin taron wanda ya samu halartar shugabannin ƙasashe da dama a Pretoria babban birnin ƙasar.
Zondo ya yi wa Ramaphosa murna inda ya kuma gabatar da shi ga baƙin da ke wurin bayan ya saka hannu a kan wata takarda, wadda ke cewa an rantsar da zabaɓɓen shugaban ƙasar.
Jama’a waɗanda ke kallo a wurin taron da gefe sun rinƙa shewa domin nuna murna bayan an rantsar da Ramaphosa.
An gudanar da addu’o’i na addinai kafin a yi rantsuwar inda malaman addinai suka yi addu’a ga sabon shugaban ƙasar da gwamnati.
‘Yan Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu sun sake zaɓar Cyril Ramaphosa a Juma’ar da ta gabata a lokacin zamansu na farko na majalisa.
Ramaphosa, wanda shi ne jagoran Jam’iyyar ANC ya samu ƙuri’u 283, inda ya kayar da Julius Malema na Economic Fighter Party wanda ya samu ƙuri’u 44.
Jam’iyyar ANC wadda ta shafe kusan shekara 30 tana mulki a ƙasar, ta mamaye siyasar ƙasar, sai dai a zaɓen da aka gudanar a bana, ta rasa rinjaye a majalisa.
Jam’iyyar ta ANC tana da ‘yan majalisa 159 a halin yanzu a majalisar ƙasar mai mambobi 400, wanda hakan ya sa lamari ne mai wuya ta iya kafa gwamnati.
Wannan ne ya sa jam’iyyar ta yi haɗala da jam’iyyu kamar su Democratic Alliance da Patriotic Alliance da Inkatha Freedom Party da sauransu.