An yada taron bikin rantsawar kai tsaye ta kafar talabijin na kasar ce ta watsa . Hoto: shafin X na Shugaban kasar Nijar 

Shugaban Mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani wanda ya dare karagar mulkin kasar bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli, ya rantsar da shugabannin hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma kotun jiha na kasar a hukumance a ranar Alhamis.

Kafar talabijin na kasar ce ta watsa taron bikin rantsawar guda biyu kai tsaye.

Sabbin shugabannin hukumar da na kotun sun yi rantsuwar fara aiki a gaban shugaban mulkin sojin kasar wato Janar Abdourahamane Tiani.

Taron na zama karo na farko da shugaban ya taba bayyana a bainar jama'a tun bayan da ya jagoranci hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Manyan hafsoshin soji da mambobin gwamnati da sarakunan gargajiya da malaman addini da kuma jami’an diflomasiyyar kasashen waje ne suka halarci bikin rantsarwar a babban birnin kasar, Yamai.

Sabuwar kotun jihar za ta maye gurbin kotun sauraron kararrakin zabe da kuma ta majalisar dokokin jiha da aka rusa bayan juyin mulkin kasar.

A yanzu haka dai gwamnatin mulkin sojin ta bukaci ta mika mulki ga farar hula nan da shekaru uku masu zuwa, sai dai ba a kayyade ranar da za a gudanar da zabe ba.

Aikin hukumar yaki da cin hanci

Babban aikin hukumar yaki da cin hanci da rashawa shi ne kwato dukiyoyin al’umma da aka ƙwace ba bisa ƙa’ida ba.

Ma'aikatan hukumar sun ƙunshi alkalai da sojoji da jami’an ‘yan sanda da kuma wakilan al’umma.

Tiani ya yi alkawarin gudanar da taron tattaunawa na kasa, wanda zai taimaka wajen sanin ainihin lokacin da za a kwashe da kuma wa'adin mika mulki za su kasance.

Bazoum dai yana tsare a gidansa da ke tsakiyar fadar shugaban kasa tun bayan hambarar da shi.

Tun bayan juyin mulkin da kungiyar ECOWAS ta ƙaƙabawa Nijar takunkumin karya tattalin arziki, abin da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki da kuma haifar da karancin wasu kayayyakin da suka hada da magunguna.

AFP