Tinubu ya taba zama gwamnan jihar Legas tsakanin 1999-2007. Hoto/Getty

An rantsar da tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sabon shugaban Nijeriya.

Alkalin Alkalan kasar Olukayode Ariwoola ne ya rantsar da shi a dandalin Eagle da ke Abuja ranar Litinin.

Kafin nan, sai da aka rantsar da tsohon gwannan jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban Nijeriya.

Sabon mataimakin shugaban kasar, wanda ya maye gurbin Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi alkawarin yin bin kundin tsarin mulkin kasar sau da kafa.

Da yake shan ratsuwar kama aiki, Shugaba Tinubu, ya yi alkawarin kyautata rayuwar 'yan kasar da inganta tsaro da kuma karfafa tattalin arziki.

“Ni, Bola Ahmed Tinubu, na yi rantsuwar cewa zan yi biyayya ga Tarayyar Nijeriya, kuma zan kare martabar kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeria. Allah ya taimake ni,” in ji Shugaba Tinubu.

Tinubu shi ne shugaban Nijeriya na 16 kuma ya maye gurbin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Jim kadan bayan Tinubu ya sha rantsuwar kama aiki, tsohon shugaban kasar Buhari ya fice daga dandalin a cikin mota kirar Jeep.

Takaitaccen bayani kan Shugaba Tinubu:

  • An haife shi a birnin Legas ranar 29 ga watan Maris na 1952
  • Ya yi digiri a fannin Nazarin Kasuwanci a Jami'ar Jihar Chicago a 1970
  • Ya shiga harkokin siyasa inda aka zabe shi a matsayin Sanata a 1992
  • Ya zama gwamnan Jihar Legas a 1999-2007

TRT Afrika