Dorinar ruwa a Kebbi

A yau Talata ne aka yi rabon naman dorinar ruwan da aka kashe a garin Yauri na Jihar Kebbin Nijeriya.

Shugaban ƙaramar hukumar Yauri Honorabul Abubakar Shu’aibu ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa a jiya Litinin ne masunta da manoman shinkafa suka kashe dorinar ruwan bisa umarnin gwamnatin jihar, bayan da ta kashe mutum ɗaya tare da jikkata wani.

An shafe makonni ana neman dorinar ruwan bayan kashe wani dattijo da ya je inda jaririn dorinar ruwan yake ba tare da saninsa ba, lamarin da ya harzuƙa ta har ta yi ajalinsa.

Honorabul Abubakar Shu’aibu ya ce duk da cewa akwai dokar hana kashe dabbobin ruwa da na daji a jihar, ya zama dole aka ɗauki wannan matakin en saboda dorinar ruwan na barazana ga rayuwar jama’a.

Ya tabbatar da cewa a yanzu haka akwai dorinar ruwa da dama a cikin kogin da ke garin Yaurin. Rahotanni sun ce al’ummar garin sun kasance cikin murna da farin cikin wannan al’amari, inda kuma suka samu namanta da aka rarraba.

“Bayan kashe ta ɗin an kai shi wajen Uban Kasar Gungu inda a can aka rarraba wa waɗanda suka kashe ta da ma sauran mutanen gari da ake sha’awar naman nata,” in ji shugaban ƙaramar hukumar.

TRT Afrika