Gwamnatin jihar Kaduna a Nijeriya ta ce an samu nasarar kawar da ‘yan bindiga da dama a ƙramar hukumar Giwa.
A sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Juma’a, ta ce an yi hakan ne bayan wasu hare-haren sama da ƙasa da dakarun rundunar Operation Whirl Punch suka kai, inda har aka samu nasarar kashe wasu daga cikin shugabannin ‘yan bindiga a wani waje da aka gano suna haɗuwa a kusa da garin Bula, a tsakanin Dajin Yadi na ƙaramar hukumar Giwan.
A cewar wani rahoto da rundunar ta bai wa gwamnatin jihar Kaduna, an kai hare-haren ne bayan samun sahihan bayanan sirri waɗanda suka biyo bayan kawar da wasu manyan ‘yan bindiga da aka yi a kan iyakar Kaduna da Katsina.
Rahoton bayanan sirrin da fari ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun haɗu ne a wani waje don yin wani taro na yadda za su kai mummunan hari a cikin yankunan da ke Dajin Yadi.
“An bi diddigin abin sosai, kuma a lokacin da aka amince, an ga ‘yan bindigar dauke da makamai suna tunkarar wurin a kan babura.
“Wani bincike da aka yi ya tabbatar da motsi da haduwar ‘yan bindigar a rukunin mutane kusan bakwai zuwa goma a wata cibiya da ke wurin.
Bayan an tantance inda aka kai harin, an tabbatar da kashe ‘yan ta’addan da dama ciki har da Alhaji Kachalla Ragas – aminin Buharin Yadi tun na ƙuruciya.
Da yake karbar rahoton, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana jin dadinsa tare da yaba wa jami’an tsaro bisa gaggauwa da daukar matakin da suka yi, da kuma kokarin da suke yi na kawar da ɓarna.
Gwamnan ya gode wa majiyoyi daban-daban da suka bayar da muhimman bayanan da suka kai ga nasarar kai hare-haren.
Daga ƙarshe gwamnatin jihar ta umarci al'ummar jihar da su dinga taimaka wa da ba da bayanai masu amfani a duk wani al'amari da ba su yarda da shi ba ta hanyar kiran layukan gaggawa na tsaro kamar haka; 09034000060 da kuma 08170189999.