Wani mazaunin yankin ya ce yawancin mutanen da suka mutu tsofaffi ne da ba za su iya guduwa ba. / Hoto: AP

Mutum aƙalla 21 ne suka mutu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya, a cewar shaidu.

Edibo Ameh Mark, shugaban ƙaramar hukumar Omala, inda lamarin ya faru, ya ce an binne mutanen da aka kashe.

Ya ƙara da cewa Fulani ne suka kashe mutanen a wani harin ramuwar gayya da suka kai bayan mazauna ƙauyen sun kashe ƴan'uwansu guda shida kwana uku da suka wuce, ciki har da biyu da aka fille wa kawuna.

Rikici tsakanin manoma da makiyaya na ci gaba da barazana a yankin saboda ƙaruwar rashin wuraren kiwo da a wasu lokuta kan sa makiyaya su shiga gonakin al'ummar gari.

"Ba mu taɓa tunanin za a kawo wannan hari ba," in ji Elias Atabo, mai shekara 54. "Maharan sun kwashe fiye da minti 45 suna harbe-harbe."

Wani mazaunin yankin mai suna Atabor Julius ya ce makiyaya kusan 100 ne suka kai hari a ƙauyensu ranar Alhamis inda suka riƙa yin harbi na kan mai-uwa-da-wabi, yana mai cewa sun gano gawarwaki 19 a lokacin da lamarin ya faru sannan aka gano ƙarin gawawwaki 15 ranar Juma'a.

Julius ya ƙara da cewa yawancin mutanen da suka mutu tsofaffi ne da ba za su iya guduwa ba.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar bai ce komai ba game da batun duk da saƙon da aka aika masa.

TRT Afrika da abokan hulda