FRELIMO ce ke mulki a Mozambique tun bayan samun 'yancin ƙasar daga Portugal a 1975. / Hoto: Reuters

Aƙalla mutum 10 ne aka kashe sakamakon zanga-zangar zaɓen shugaban ƙasa na 9 ga watan Oktoba a Mozambique, zaɓen da ɗan takarar Jam’iyyar FRELIMO wato Daniel Chapo ya yi nasara.

Wata ƙungiya mai zaman kanta ta CIP ta ƙasar, ta ce an samu labarin mace-mace a sassa daban-daban na ƙasar bayan tashe-tashen hankula da suka faru bayan zaɓen ƙasar, sakamakon zanga-zangar da matasa suka yi.

Maputo babban birnin ƙasar Mozambique ya sha da ƙyar a ranar Alhamis a zanga-zangar bayan da aka ayyana Chapo a matsayin wanda ya lashe kusan kashi 71 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Jam'iyyar FRELIMO ce ke mulki a Mozambique tun bayan samun 'yancin ƙasar daga Portugal a 1975.

An ƙona ofishin Jam'iyyar FRELIMO

Ɗan takara mai zaman kansa Venancio Mondlane, mai goyon bayan masu fatan ci gaban Mozambique (PODEMOS), shi ya zo na biyu da kashi 20 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Ɗan takarar babbar jam'iyyar adawa Ossufo Momade na jam'iyyar RENAMO ya zo na uku da kusan kashi 6 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Kafofin yaɗa labaran Mozambique sun ruwaito cewa masu zanga-zangar sun ƙona ofisoshin jam'iyyar FRELIMO mai mulki uku, yayin da aka fasa shaguna da dama aka sace kayayyaki tare da ƙona motoci.

An kama ɗaruruwan mutane, inda alƙaluman 'yan sanda ke nuna cewa mutum 20 ne suka jikkata yayin wannan zanga-zanga.

Shugaban ƙasa ya buƙaci a zauna lafiya

'Yan sanda sun kuma ce aƙalla jami'ai takwas ne suka jikkata a zanga-zangar, kuma an fara shari'ar masu laifi 44 da ake zargi.

An tilasta wa 'yan sanda jefa hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa zanga-zangar, wadda ta samo asali daga zargin maguɗin zaɓe da aka yi domin goyon bayan jam'iyya mai mulki. Tuni dai ƙungiyar ta RENAMO ta yi kira da a soke sakamakon zaɓen.

Jami'an tsaro a Mozambique har yanzu ba su bayar da alƙaluman adadin waɗanda suka mutu a hukumance ba, sai dai kafafen yaɗa labarai da dama a Mozambique sun bayar da rahoton cewa an samu asarar rayuka a zanga-zangar da ake ci gaba da yi.

Shugaban Mozambique mai barin gado Filipe Nyusi, wanda ya gama kammala wa'adinsa na biyu, ya buƙaci 'yan ƙasar su kwantar da hankalinsu kafin bayyana sakamakon zaɓen.

TRT Afrika