Wani harin ‘yan tada kayar baya a babban birnin kasar Mali wanda aka yi nufin kai wa sansanin horar da ‘yan sandan soji da filin jirgin sama ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 70 tare da raunata wasu 200, daya daga cikin mafi muni da jami’an tsaro suka gani a shekarun baya.
Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutane 77 ne suka mutu yayin da wasu 255 suka samu raunuka a hare-haren na ranar Talata a birnin Bamako.
Ingantacciyar takarda ta sirri ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 100, inda ta bayyana sunayen mutane 81 da abin ya shafa.
Jaridar Le Soir ta ranar Alhamis ta ruwaito cewa za a yi jana'izar daliban 'yan sandan soji kusan 50 a ranar.
Na farko irinsa a cikin shekaru
Kawo yanzu dai hukumomin sojin Mali ba su fitar da takamaiman adadin wadanda suka mutu sakamakon harin ba, wanda kungiyar JNIM mai alaka da Al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin.
Wannan hari dai shi ne irinsa na farko cikin shekaru da dama da suka gabata, kuma ya kada hantar cikin gwamnatin mulkin soja, kamar yadda masana suka ce.
Babban birnin kasar Mali dai ya tsallake rijiya da baya daga hare-haren da ake kai wa akai-akai a wasu sassan kasar da ke Yammacin Afirka.
Babban hafsan sojin ya yarda da yammacin ranar Talata cewa "an yi asarar wasu rayukan mutane", musamman ma'aikata a cibiyar 'yan sanda ta sojoji.
Juya wa ECOWAS baya
JNIM ta yi iƙirarin cewa wasu ƙalilan daga cikin mayakanta sun kashe tare da raunata “daruruwa” daga bangaren hamayya, ciki har da mambobin ƙungiyar sa-kai na Rasha Wagner.
Harin dai ya zo ne kwana guda bayan da kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso karkashin jagorancin mulkin soja suka cika shekara guda da kafa kungiyarsu ta kawancen kasashen Sahel (AES).
Ƙasashen uku, wadanda ke karkashin mulkin soji tun bayan juyin mulkin da aka yi ta yi tun shekara ta 2020, sun karya alaka da tsohuwar ‘yar mulkin mallaka ta Faransa inda suka karkata a fagen soji da siyasa zuwa sauran abokan hulda da suka hada da Rasha.