Hukumar IOM ta ƙara da cewa mutum 100 kuma sun ji jikkata yayin da aka bayar da rahoton ɓatan mutum 300. / Photo: Reuters

Aƙalla mutum 700 aka kashe a Yammacin Darfur sakamakon arangama da aka yi tsakanin dakarun rundunar sojin Sudan da na rundunar sa-kai ta RSF a garin El Geneina a ranakun Asabar da Lahadi, 4 zuwa 5 ga watan Nuwamba, a cewar wata sanarwa ta Hukumar Ƙaura ta Duniya (IOM).

Hukumar IOM ta ƙara da cewa mutum 100 kuma sun jikkata yayin da aka bayar da rahoton ɓatan mutum 300, in ji sanarwar wacce aka fitar a ranar Alhamis.

Lalacewar lamari a yankin Darfur

Daruruwan mutane ne ke yin ƙaura daga yankin Darfur na Sudan a watannin baya-bayan nan ba tare da ɗaukar wasu kayyayaki ba sosai. Abin da mutane da yawa ke fita da shi, shi ne baƙin ciki.

Waɗanda suka isa garin Adre da ke kan iyakar ƙasar Chadi sun ba da rahoton ƙaruwar kashe-kashen mutane a yammacin Darfur.

Mutane da yawa suna samun labarin 'yan uwansu daga sabbin ƴan hijira. Asiya, wacce ta gudu ita da mahaifiyarta da ‘ya’yan ‘yar uwarta, ta ce an gaya mata ɗan uwanta ya rasu. Kuma ba su iya samun mahaifinta ba.

Suka ƙona komai suka kwashe komai. Ba mu zo da komai ba. Allah ne kaɗai ke tare da mu sai tufafinmu."

Yaƙi tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na Rapid Support Forces (RSF) ya sake haifar da rikicin ƙabilanci a yankin Darfur.

Sansanin soji

A cikin watan Satumba, babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya ce RSF da mayaƙan sa-kai na ƙawance sun kashe ɗaruruwan mutane daga al'ummomin Masalit.

A baya 'yan bindiga sun musanta cewa suna kai hare-hare na ƙabilanci kuma ƙungiyar ta RSF ta ce ba ta da hannu a abin da ta bayyana a matsayin rikicin ƙabilanci.

Mafi yawan ƴan gudun hijirar mata ne da yara, a cewar ƙungiyar MSF.

A cikin makon da ya gabata ƙungiyar RSF ta karɓe babban sansanin sojojin da ke El Geneina babban birnin jihar Darfur ta Yamma.

Uku daga cikin waɗanda ke tserewa zuwa ƙasar Chadi sun ce sun shaida kashe-kashen da ƴan bindiga da mayaƙan RSF suka yi wa Masalit a Ardamata.

Wata gGunduma ce da ke bayanta inda sansanin sojoji da sansanin 'yan gudun hijira suke.

Rundunar RSF ba ta ce komai a a kan buƙatar Reuters ta yin magana da ita.

Fashi

Nabila Abdel Rahman ta ce ana kashe mutane da raba su da muhallansu a Ardamata.

"Ana yi wa yara da mata kisan gilla da ƙwace musu kuɗaɗe da duk abin da suka mallaka, kuma ba za su iya tserewa ba."

Wasu mata na kuka bayan samun labarin mutuwar ƴa'uwansu a lokacin da suke jiran isarsu Chadi don su haɗu. Hoto: Reuters

Yaƙin Sudan ya rutsa da sama da mutum miliyan shida. Fiye da rabin miliyan daga cikinsu ne suka tsallaka zuwa ƙasar Chadi, a cewar hukumar kula da baƙin haure ta duniya. Amma da alama sabon tashin hankalin ya haifar da ƙaruwar hakan sosai.

Ƙungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres ta ce ƴan gudun hijira da dama sun sake isa wajen a kwanaki ukun farko na watan Nuwamba fiye da waɗanda suka shiga a baki ɗayan watan da ya gabata na Oktoba.

Hakan na nufin kusan mutum 7,000 kenan wadanda mafi yawansu mata da yara ne, masu ɗauke da labaran irin masifar da suka shiga a dalilin faɗan da ke shafar fararen hula, a cewar ƙungiyar agajin ta lafiya.

TRT Afrika da abokan hulda