Jami'an tsaron Nijeriya sun ce suna samun nasara a kan 'yan ta'adda, duk da cewa lamarin yana karuwa a kullum. Hoto: Reuters

Kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Nijeriya ya bayyana cewa mutum 9, 734 sun rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanci a fadin kasar a shekarar 2023.

A wani rahoto na musamman da kamfanin ya fitar, ya yi kididdiga dangane da kiyasin ayyukan ta’addanci da aka yi a kasar tun daga farkon shekarar har zuwa karshenta.

A watanni shidan farko na shekarar, kamfanin ya ce mutum 4,574 sun rasa rayukansu inda aka sace mutum 1,489 a hare-hare 2,512.

Sannan a watanni shida na karshen shekarar mutum 5,160 ne suka rasu sannan aka sace 2,560 a hare-hare 4,003.

Mace-mace

Kamfanin na Beacon Consulting ya yi kididdigar mace-macen da aka samu dangane da yankunan Nijeriya.

- A Arewa ta Tsakiyar Nijeriya mutum 1,114 ne suka rasu a watanni shidan farkon shekarar, sannan mutum 888 suka rasu bayan nan.

- A Arewa Maso Gabashin Nijeriya mutum 1,375 ne suka mutu a watanni shidan farkon shekarar, sannan mutum 2,037 suka rasu bayan nan.

- Sannan a Arewa Maso Yammacin Nijeriya mutum 1,126 suka rasu a watannin farkon shekarar sannan 1,164 a watannin karshen shekara.

- A Kudu Maso Gabashin Nijeriya kuwa mutum 319 ne suka rasu a watanni shidan farko sannan 239 suka rasu a watannin shidan karshe.

- A Kudu Maso Kudancin Nijeriya mutum 280 suka rasu a watannin shidan farkon shekarar sannan 418 suka rasu a watannin shidan karshe duk a sakamakon ta’addanci.

Garkuwa da mutane

Dangane da batun garkuwa da mutane a 2023, kamfanin na Beacon Consulting ya fitar da ƙididdiga dangane da wadanda aka sace a 2023.

- A Arewa Maso Tsakiyar Nijeriya, mutum 1,006 aka yi garkuwa da su a yankin.

- Sannan kuma a Arewa Maso Gabashin Nijeriya, mutum 795 aka sace a yankin.

- Haka kuma a Arewa Maso Yammacin Nijeriya, mutum 1,728 aka sace a yankin.

- Sai kuma a Kudu Maso Gabashin Nijeriya, mutum 165 aka sace a yankin.

- A Kudu Maso Yammacin Nijeriya kuwa, mutum 169 ne aka sace a yankin.

- Sai kuma a Kudu Maso Kudancin Nijeriya, mutum 186 aka sace a yankin.

TRT Afrika