Wannan harin na daga cikin jerin hare-haren da aka kai a ƙasar da ke fama da yaƙin basasa a daidai lokacin da rikicin ƙasar ke ƙara ta’azzara. / Hoto: Reuters

Kimanin mutum 70 ne aka kashe a wani hari da aka kai a asibiti ɗaya tilo da ke aiki a birnin El Fasher wanda aka yi wa ƙawanya da ke arewacin Darfur a Sudan, kamar yadda babban jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya ya bayyana a ranar Lahadi. T

Tedros Adhanom Ghebreyesus, wanda shi ne shugaban na WHO ya bayyana cewa baya ga kimanin mutum 70 da suka rasu, akwai wasu mutum 19 da suka jikkata.

Gwamnan Darfur Mini Minnawi ya bayyana cewa an kai hari asibitin ne ta hanyar amfani da jirgi maras matuƙi.

Wannan harin na daga cikin jerin hare-haren da aka kai a ƙasar da ke fama da yaƙin basasa a daidai lokacin da rikicin ƙasar ke ƙara ta’azzara.

Harin da aka kai a asibitin koyarwa na mata masu juna biyu na Saudiyya, wanda jami'an yankin suka ɗora alhakinsa kan dakarun Rapid Support Forces, ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyar ke fuskantar rashin nasara a ‘yan kwanakin nan a fagagen daga daban-daban karkashin jagorancin babban hafsan sojin kasar Janar Abdel-Fattah Burhan.

Rashin nasarar ta haɗa da ƙona ganin Burhan da aka yi a wani bidiyo a wata matatar mai da ke ƙonewa a arewacin Khartoum a ranar Asabar inda dakarun nasa suka ce sun ƙwace ta daga hannun RSF.

Reuters