Yankunan da ke kan iyaka tsakanin Nijar da Mali da Burkina Faso sun kasance mafakar 'yan ta'adda da ke da alaƙa da Daesh da Al Qaeda, waɗanda suka yi yaƙi da gwamnati. / Hoto: Reuters

Aƙalla mutum 39 aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Nijar kusa da iyaka da Burkina Faso a 'yan kwanakin nan, kamar yadda ma'aikatar tsaro ta Nijar ɗin ta tabbatar.

"Wasu munanan bala'i guda biyu sun faru a cikin al'ummomin Libiri da Kokorou, masu aikata laifuka waɗanda ayyukan jami'an tsaro suka takurasu sun kaddamar da hare-hare kan fararen hula marasa makamai," in ji ma'aikatar tsaro a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

Hare-haren sun faru ne a tsakanin 12 zuwa 14 ga watan Disamba, kamar yadda sanarwar ta bayyana ba tare da bayar da bayanai kan lokutan da hare-haren suka faru ba.

Munanan hare-hare

Al'ummomin suna yankin iyakar Tera, yankin da ke cike da mayaka wanda ya fuskanci hare-haren 'yan bindiga musamman a 'yan kwanakin nan.

Yankunan da ke kan iyaka tsakanin Nijar da Mali da Burkina Faso sun kasance mafakar 'yan ta'adda da ke da alaƙa da Daesh da Al Qaeda, waɗanda suka yi yaƙi da gwamnati.

Daya daga cikin hare-hare na baya-bayan nan da 'yan bindigar suka kai sun kashe fararen hula 21 a wani hari da suka kai kan ayarin kayayyaki, in ji majiyoyin kasar a ranar 7 ga watan Disamba.

AFP